Lokaci Ya Yi: Tsohon Babban Jami'in Sojin Najeriya kuma Jigon APC Ya Rasu
- Tsohon jami'in rundunar sojin saman Najeriya, AVM Terry Omatsola Okorodudu ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 70 da haihuwa
- Okorodudu, wanda jigo ne a jam'iyyar APC ya mutu ne ranar Talata bayan fama da doguwar jinya a birnin Nairobi na kasar Kenya
- Ana ganin rasuwar dattijon babban rashi ne ga rundunar soji da Najeriya baki daya saboda irin gudummuwar da ya bayar a rayuwarsa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Najeriya ta rasa daya daga cikin tsofaffin jami'an rundunar sojin sama, wadanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa kasa hidima kafin su yi ritaya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa tsohon jami'in rundunar sojin saman Najeriya, wanda ya kai matsayin Air Vice Marshal (AVM) kafin ya yi ritaya, Terry Omatsola Okorodudu ya rasu.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa AVM Okorodudu (mai ritaya) ya rasu ne bayan fama da doguwar rashin lafiya a birnin Nairobi na kasar Kenya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon jami'in sojin sama ya rasu
Bayanai sun nuna cewa marigayin ya cika ne a ranar Talata, 9 ga watan Satumba, 2025 yana da shekaru 70 a duniya.
An haifi AVM Okorodudu mai ritaya, a ranar 27 ga Agusta, 1955 a birnin Fatakwal na jihar Ribas da ke Kudancin Najeriya, amma dan asalin jihar Delta ne.
Ya shiga rundunar sojin saman Najeriya a Kaduna inda ya fara horo tare da sauran sababbin jami’ai.
Bayan shekaru masu tsawo na jajircewa, sadaukarwa da kuma nuna kwarewa a harkar soja, ya kai matsayin Air Vice Marshal watau AVM.
Daga wannan matsayi ne AVM Okorodudu ya yi ritaya a shekarar 2010 bayan kammala fiye da shekaru 30 yana bauta wa kasa.
AVM Okorodudu ya nuna sha'awar takara a APC
A gefe guda kuma, Okorodudu ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar sanatan Delta ta Kudu karkashin inuwar jam'iyyar APC.
Sai dai duk da ya bayyana aniyarsa ta takara, tun kafin zaben fitar da gwanin APC a mazabar ya canza shawara, ya janye daga neman kujerar sanatan.

Kara karanta wannan
'Talauci ya yi muni a Najeriya,' El Rufa'i ya ce akwai mafita kan matsin tattalin arziki
Ana ganin dai mutuwar mutum irin AVM Okorodudu babban rashi ne ga rundunar sojin saman Najeriya, jihar Delta da ma kasa baki daya.
An tattaro cewa za a ci gaba da tunawa da shi saboda kasancewarsa mutum mai gaskiya, biyayya da kuma nuna kishin kasa wanda zai wahala a manta da gudummuwarsa.
Yanzu haka, iyalinsa, abokai da kuma abokan aiki suna cikin jimami, yayin da ake jiran sanarwar daga danginsa game da shirye-shiryen jana’izarsa.
Tsohon dan takarar gwamnan Ondo ya rasu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon dan takarar gwamna a jihar Ondo karkashin inuwar jam'iyyar SDP, Otunba Bamidele Akingboye ya riga mu gidan gaskiya.
Iyalan marigayin ne suka tabbtar da hakan a wata sanarwa da suka fitar, sun ce ya rasu ne a gidansa da ke cikin Legas.
Jam'iyyar SDP ta yi alhinin wannan rashi, tana mai bayyana marigayi Bamidele Akingboye a matsayin shugaba na gari wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
