An Nada Farfesa Maqari Limami a Masallacin Ka’abah? Malamin Ya Yi Karin Haske
- Wasu daga cikin mutane sun yi ta yadawa a kafafen sada zumunta cewa an nada Farfesa Ibrahim Maqari a matsayin limamin masallacin Ka’abah
- Sai dai Farfesa Maqari ya fito a yau Laraba, 10 ga Satumba 2025 inda ya yi karin haske kan rahoton da ake ta yadawa a kafofin sadarwa ta zamani
- Malamin ya musanta rahoton, yana mai jaddada cewa kwata-kwata ba gaskiya ba ne, tare da kira ga jama’a su guji yada labaran ƙarya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - An yi ta yada wasu rahotanni game da nada malami a Najeriya a matsayin limami a masallacin ka'abah.
Mutane da dama sun sanar da cewa an nada babban limamin masallacin Abuja, Farfesa Ibrahim Makari a matsayin daya daga cikin limaman ka'abah.

Source: Facebook
Maqari ya magantu kan nada shi liman a ka'abah
Farfesa Maqari ya yi karin haske kan rahoton da ake yadawa a yau Laraba 10 ga watan Satumbar 2025 a shafin Facebook.
Malamin wanda dan asalin jihar Kaduna ne yana daga cikin manyan limaman masallacin Abuja da ke Najeriya.
Sheikh Maqari ya yi rubutu musamman a shafinsa inda ya musanta labarin da cewa kwata-kwata ba gaskiya ba ne.
Farfesan ya musanta labarin a cikin rubutun da ya yi wanda ke tabbatar da cewa bai san ma da maganr nadin nasa ba.

Source: UGC
Martanin Maqari kan nada shi liman a ka'abah
Farfesa Maqari ya fara rubutu da cewa 'labarin karya ne' kafin daga bisani ya kwafi abin da ake yadawa da kuma yada shi a kasa.
Malamin ya ce:
"Labarin karya ne.
"Alhamdulillah, godiya ta tabbata ga Allah, kwamitin da ke da alhakin nada sababbin limaman Masallacin Ka’aba ya zabi ɗan Afirka Baƙar fata karo na farko, Babban Limamin Masallacin Ƙasa a Abuja, Farfesa Sheikh Ibrahim Makari a matsayin ɗaya daga cikin limaman Masallacin Harami a Makkah.
"Wannan babbar nasara ce a tarihi kuma abin alfahari ga Musulmi a Najeriya, Afirka, da ma duniya baki ɗaya.
"Muna ƙarfafa dukkan Musulmi da su taya murnar wannan ni’ima ta hanyar yin addu’o’in alheri ga Sheikh Ibrahim Makari tare da yaɗa wannan labari domin sauran su samu damar taya murna da yin addu’a.
"Allah ya sanya wannan mukami ya zamo abin alheri ga Musulman Najeriya, Afirka, da dukkan al’ummar Musulmi gaba ɗaya. Ameen."
Maqari yana shirin hada kan malaman Musulunci
Mun ba ku labarin cewa tawagar Malamai da kungiyoyi ƙarƙashin jagorancin Farfesa Ibrahim Maqari ta kai ziyara ga manyan malaman addini a Najeriya.
An jaddada cewa haɗin kan Musulmi ba yana nufin barin mazhaba ko fahimta ba ne, illa kawar da husuma da kafirta juna wanda ke kara kawo rashin fahimta a tsakani.
Malaman da aka ziyarta sun nuna goyon baya ga wannan yunƙuri na samar da murya guda ga al’ummar Musulmi sai dai akwai wasu malamai da dama sun yi wasti da shirin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

