Prof Makari ya janye karar da ya shigar kan Dr Gadon Kaya, ya bayyana dalili

Prof Makari ya janye karar da ya shigar kan Dr Gadon Kaya, ya bayyana dalili

  • Farfesa Ibrahim Makari ya janye karar da ya shigar kan Dr Abdallah Gadon Kaya a kwanakin nan
  • A baya Farfesa ya maka Dr a kotu ne bisa zarginsa da bata masa suna tare da fadin maganganu akansa
  • Farfesa a wani bidiyo da muka samo ya bayyana dalilai da suka sanya ya janye karar da a shigar

Abuja - Malamin addinin Islama, limamin masallacin kasa dake babban birnin tarayya, Abuja, Farfesa Ibrahim Makari, ya bayyana janye karar da ya shigar kan Dr Abdallah Gadon Kaya dake jihar Kano kan zargin ya bata masa suna.

Malamin ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo da Legit.ng Hausa ta samo a yayin wani karatu da yake gabatarwa, inda ya bayyana dalla-dalla dalilan da yasa ya janye karar.

Kara karanta wannan

Ya kamata sojoji su zage dantse: Buhari ya yi martani mai zafi kan harin NDA

Idan zaku iya tunawa, Makari ya shigar da kara ne, inda ya nemi kotu ta bi kadunsa bisa wasu maganganu da Gadon Kaya ya furta akansa, wadanda Makari ya dangantasu da bata suna.

Farfesa Makari ya janye karar da ya shigar kan Sheikh Gadon Kaya, ya bayyana dalili
Farfesa Ibrahim Makari | Hoto: taskarlabarai.com
Asali: Twitter

Manyan Najeriya ne suka sanya ni janye karar

Bayan da aka kai takardar kara ga Dr Gadon Kaya, malamin ya ce wasu manya a Najeriya, kuma masu fada a ji sun jawo hankalinsa, kuma sun nemi lallai ya janye karar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Manya a kasar nan, sun shigo sun nemi, su a bar musu shari'ar. Ma'ana su za su yi shari'ar kar a yi a kotu. Kuma cikinsu akwai shugaban hukumar tsaro na kasa gaba daya, da wasu. Na fada musu cewar zan sanar sunce ba laifi in sanar...
"Kuma abin ya shafi har iyaye har da mahaifina duk sun amince a kan hakan, sun zabi hakan. Saboda haka, dalilin haka sun ce su a barsu za su nemi wannan mutumin da yayi maganganu ya fito da hujjar da yace yana dashi su ya basu hujjar.

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalami: Ya kamata a sake zage dantse a nemo mafita ga tsaron kasar nan

"Idan bai da hujja za su nemi ya rubuta a rubuce cewar ba shi da hujja."

Makari ya jaddada hakan da cewa, ya amince da bukatarsu kasancewarsu iyaye, kuma masu fada a ji ba wai a kansa kadai ba, a kasa baki daya.

Kotu ta tsare mutane 8 da ake zargi da yin garkuwa da matar kwamishinan

A wani labarin, Wata kotun majistare da ke Makurdi ta bayar da umurnin a ci gaba da tsare wasu mutane takwas a gidan yarin jihar bisa zarginsu da yin garkuwa da Ann Unenge, matar kwamishinan filaye, bincike da ma’adanai na jihar Benue.

Wadanda ake zargin sune Samuel Ogbodo, Chidi Anekwe, Monday Anyigor, John Igwe, John Nwoke, Mathias Odoh, Matthew Eze da Iorhemen Yagba, The Cable ta ruwaito.

An tuhume su da laifin hada baki, fashi da makami da ta’addanci, wadanda laifuka ne da suka saba da tanadin sassan daban-daban na dokoki na musamman na jihar Benue.

Kara karanta wannan

Farfesa Aminu Dorayi: Bakanon da ya tuko motarsa daga Landan har zuwa Kano

Adah Odeh, alkalin kotun, ya ba da umurnin a ci gaba da tsare su a cibiyar gyaran hali ta tarraya, har zuwa lokacin da za a yankje shawara kan shari’ar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: