Tinubu: Sai da Rajistar Haraji za a Yi Hulda da Banki a Najeriya daga 2026

Tinubu: Sai da Rajistar Haraji za a Yi Hulda da Banki a Najeriya daga 2026

  • Sabuwar dokar haraji da za ta fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026, za ta sauya tsarin yadda mutane ke mu'amala da banki
  • Dokar ta rusa hukumar FIRS tare da kafa NRS domin tabbatar da bin doka da oda wajen tattara haraji a fadin kasa
  • Gwamnatin Najeriya ta ce manufar ita ce faɗaɗa harajin ƙasa, rage dogaro da man fetur, da samar da kudin ayyukan cigaba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya riga ya rattaba hannu kan sabuwar dokar haraji, wacce za ta fara aiki a shekarar 2026.

Dokar ta wajabta cewa babu wanda zai iya budewa ko gudanar da asusun banki, kasuwanci, ko wani nau’in hulɗar kuɗi ba tare da rajistar biyan haraji ta TIN ba.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan lokacin fara biyan harajin fetur

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Rahoton This Day ya nuna cewa gwamnati ta ɗauki matakin a matsayin hanyar gyara tsarin tattalin arzikin ƙasa da dogaro kan al’ummarta wajen samar da kudin shiga.

Dalilin da ya sa dokar ta zama tilas

Najeriya na da ɗaya daga cikin ƙasashen da ke da raunin biyan haraji a duniya, duk da kasancewarta babbar tattalin arziki a Afirka.

Yanzu haka, mutane miliyan 10 ne kacal ke da rajistar haraji daga cikin jama’a sama da miliyan 200, yayin da masu asusun banki suka haura miliyan 60.

Talabijin TVC ya nuna cewa gwamnatin tarayya na ganin wannan gibin ya haifar da yawaitar bashi da kuma gaza gina manyan ayyuka.

Sabuwar dokar na nufin kowane ɗan ƙasa da ke hulɗar kuɗi zai shiga tsarin haraji domin rage dogaro da man fetur.

Yadda dokar za ta shafi 'yan Najeriya

Sabuwar dokar haraji ta shugaba Bola Tinubu ta ƙunshi sauye-sauye masu muhimmanci da suka shafi masu biyan haraji kamar haka:

Kara karanta wannan

Amsoshin tambayoyi 7 kan harajin fetur na 5% da za a kawo a Najeriya

  • Ba za a iya buɗewa ko gudanar da asusun banki ba tare rajistar haraji ba
  • Dukkan kamfanoni, manya da ƙanana, dole su yi rajista
  • Hukumomin gwamnati za su riƙa buƙatar rajistar haraji kafin shiga kowace yarjejeniya
  • Kamfanonin ƙasashen waje ba za su yi hulɗa a Najeriya ba tare da rajista da NRS ba
  • Cibiyoyin kuɗi ba za su yi hidima ga kowa ba sai da rajistar haraji

Tasirin wannan sauyi ga Najeriya

Masu sharhi sun bayyana cewa wannan gyara zai tilasta manyan kamfanoni, ciki har da na ƙasashen waje, su biya haraji.

An jima ana zargin cewa kamfanonin da ke amfana da albarkatun Najeriya da kayayyakin more rayuwa na kaucewa biyan haraji yadda ya kamata.

Ana ganin idan aka aiwatar da wannan tsarin yadda ya dace, za a samu karin kudin shiga da za su ba gwamnati damar rage bashi da sauransu.

Bayani kan dokar harajin fetur na 5%

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan harajin man fetur na 5% da ake shirin kawowa.

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa ba a sanya lokacin da za a fara karbar harajin ba kamar yadda wasu ke cewa za ta fara aiki a 2026.

Saboda yawan magana kan dokar ne Legit Hausa ta tattaro tambayoyi da amsoshi har bakwai game da harajin domin sanin yadda lamura ke tafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng