"Ina kan Bakata," Abba Gida Gida Ya Yi Maganar Yadda Ya Tsira da Kujerarsa

"Ina kan Bakata," Abba Gida Gida Ya Yi Maganar Yadda Ya Tsira da Kujerarsa

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ƙalubalen da ya fuskanta bayan zaben 2023 ya ƙara masa ƙaimi wajen inganta rayuwar jama'a
  • Ya jaddada cewa yana sane da alƙawarin da ya ɗauka na kawo canji mai kyau a rayuwar Kanawa a lokacin da yake kamfen
  • Gwamnan ya faɗi sabon shirinsa wajen gyara halayyar matasa, musamman mata masu ta'ammali da ƙwayoyi a jihar Kano

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa ya fuskanci ƙalubale da dama bayan zaɓen 2023.

Ya ce waɗannan wahalhalu da ƙalubale sun ƙara masa azama kan tsayin daka a kan manufarsa ta kawo canji ga jihar domin al’ummarta.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce yana sane da mutanen Kano
Hoton gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

'Talauci ya yi muni a Najeriya,' El Rufa'i ya ce akwai mafita kan matsin tattalin arziki

Abba Gida Gida ya jaddada manufarsa

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce faɗi tashin da ya biyo bayan zaben 2023 ya tabbatar masa cewa samun mulki ba abu ne mai sauki ba.

Ya bayyana haka ne a jawabinsa a wajen kaddamar da Majalisar Shura a Fadar Gwamnati ta Kano a ranar Litinin.

Ya ce:

“Na shiga cikin mawuyacin yanayi bayan zaɓen 2023, amma duk da ƙalubalen, na tsaya kan hidima ga mutanen Kano."
"Na tsinci kaina a wannan kujera ne da ikon Allah, ba ikon wani mutum ba."

“Allah ne ke bayar da mulki," Gwamna Abba

Gwamnan ya jaddada cewa duk da kiyayyar wasu mutane, amma Allah Ya ƙaddara shi ya zama gwamna a 2023, kuma Shi kaɗai zai iya yanke makomarsa a 2027.

Ya ce:

“Shugabanci ba na hannun mutum ya ke ba, Allah ne ke ba da mulki, kuma Shi ne ke cirewa idan Ya so."

Kara karanta wannan

"Ku tashi ƴan Najeriya," Atiku ya zaburar da jama'a kan kisan kiyashin Boko Haram

Ya ce abin da ya dace da adalin shugaba shi ne ya mai da hankali kan ayyukan da za su inganta rayuwar al’umma ba wai son kai na siyasa ba.

Gwamnan Kano ya ce zai yi aiki kafin 2027
Hoton gwamna Abba Kabir Yusuf yana jawabi a wani taro Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Ya ce:

“Ko zan sake neman tazarce ko ba zan nema ba, aikina shi ne in ci gaba da aiwatar da abubuwan da za su amfani talakawa."

Ya ƙara da cewa:

“Na san wata rana zan bar wannan kujera. Wannan ne yasa nake ƙoƙari a yau domin sauya Kano ta kowace fuska."

Ya nuna damuwa kan matsalolin matasa, inda ya ce shaye-shaye, ta’addanci da miyagun dabi’u na barazana ga makomarsu.

Don magance hakan, gwamnan ya sanar da kafa sabuwar cibiyar gyaran mata masu fama da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi da sauran matsalolin zamantakewa.

Ya kuma roƙi malamai su yi amfani da tasirinsu wajen tallafa wa gwamnati a wannan tafiyar gyara.

Kano: Abba zai ƙaddamar da Majalisar Shura

A wani labarin, mun wallafa cewa gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa tana fatan majalisar shura da ta kafa za ta taimaka wajen inganta ayyukanta da rayuwar Kanawa.

An gudanar da taron kaddamar da majalisar a gidan gwamnatin Kano a karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf a ranar 8 ga watan Satumba, 2025 inda ake sa ran za ta rika ba da shawari.

Kara karanta wannan

Yaron El Rufa'i: Uba ya yi raddi ga kalamai da zarge zargen tsohon Gwamnan Kaduna

Majalisar Shura ta ƙunshi manyan mutane daga bangarori daban-daban na al'umma da su ka haɗa da Farfesa Shehu Galadanci a matsayin shugabanta sai wasu sauran malamai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng