Yadda Za Ka Lissafa harajin da Za Ka Biya Gwargwadon Kuɗin da Kake Samu a Najeriya

Yadda Za Ka Lissafa harajin da Za Ka Biya Gwargwadon Kuɗin da Kake Samu a Najeriya

  • Taiwo Oyedele ya bayyana cewa sababbin dokokin haraji sun zo da tsarin zai saukaka wa yan Najeriya wahalhalu
  • Shugaban kwamitin shugaban kasa kan gyaran harajin ya yi bayanin yadda kowa zai lissafa adadin kudin da za cire masa na haraji
  • Mista Oyedele ya ce masu dibar albashi kasa da N100,000 ba za su biya ko kwandala a matsayin haraji ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban kwamitin shugaban kasa kan manufofin kudi da gyaran haraji, Taiwo Oyedele, ya kara kwantar da hankulan yan Najeriya kan sababbin dokokin haraji.

Oyedele ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa sababbin dokokin da gwamnati ke shirin aiwatarwa za su rage nauyin haraji da jama’a ke dauka, sabanin yadda ake yadawa.

Taiwo Oyedele.
Hoton shugaban kwamitin gyaran haraji na shugaban kasa, Taiwo Oyedele Hoto: @taiwooyedele
Source: Twitter

Taiwo Oyedele ya bayyana hakan ne a hirarsa da tashar Channels TV ranar Talata, 8 ga watan Satumba, 2025.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan lokacin fara biyan harajin fetur

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda za ku duba harajin da za ku biya

Ya ce kashi 97 zuwa 98 cikin 100 na ’yan Najeriya ba za su biya haraji ba kwata-kwata ko kuma za su biya kasa da abin da suke biya a yanzu idan sauye-sauyen suka fara aiki.

Ya ce kwamitinsu ya kirkiro wata na’urar lissafin haraji ta yanar gizo da ke ba wa kowa damar shigar da bayanan kudinsa don sanin yawan harajin da zai biya yanzu da kuma a karkashin sabon tsari.

"Mun sanya na'uarar a shafinmu na yanar gizo, mutum zai iya shiga akwai QR Code da zai dauki hoto da wayarsa, daga nan ka sanya kudin shigarka, za ta nuna maka harajin da za ka biya.
“Idan kana dibar albashin N100,000 a wata ko kasa da haka, to baka cikin wadanda za su rika biyan harajin kudin shiga daga watan Janairu. Wannan ma ya fi mafi karancin albashi.”

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun badda kama yayin tafka ta'asa a Zamfara

Wane sauki za a samu wajen biyan haraji?

Ga masu matsakaicin karfi kuwa, wadanda ke samun N1.8m zuwa N1.9m a shekara, Oyedele ya ce za a rage masu harajin da suke biya.

A cewarsa, mataki na uku shi ne na masu arziki, su kuma za a kara musu yawan kudin harajin da suke biya bisa tsarin da ake amfani da shi a duk duniya.

A bangaren kamfanoni kuma, ya ce gwamnati ta dauki matakin tallafa wa ’yan kasuwa musamman kanana da matsakaita, in ji Leadership.

“A da, idan jarin kasuwanci ya kai N25m, za ka biya haraji. Amma yanzu an daga matakin zuwa N100m. Idan kasuwancinka bai wuce N100m ba a shekara, ba za ka biya komai ba.”
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Hoton shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Matsalolin da dokokin haraji za su magance

Oyedele ya kara da cewa daya daga cikin manyan abubuwan da sabon tsari zai magance shi ne matsalar biyan haraji kala daban-daban wadda ta dade tana damun Najeriya.

Sababbin sauye-sauyen, a cewarsa, na da nufin kare talakawa, rage nauyi ga ma’aikata, da kuma karfafa gwiwar masu kasuwanci don bunkasa tattalin arzikin kasa.

Kara karanta wannan

"Ba ruwan Tinubu," An jingina harajin fetur da gwamnatin marigayi Umaru Yar'adua

Oyedele ya ce Yar'adua ya kawo harajin fetur

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kwamitin gyaran haraji na shugaban kasa ya ce ba gwamnatin Bola Tinubu ta kafa dokar biyan harajin fetur ba.

Oyedele ya ce tun shekarar 2007, gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Marigayi Umaru Musa 'Yar'adua ta kirkiro harajin 5% kan kowace litar fetur.

Ya ce tun da aka kafa dokar a shekarar 2007, amma ba a taba aiwatar da ita ba saboda gwamnatin wancan lokacin na bayar da tallafin mai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262