'Buhari Ya Yi Barazanar Tsige Ni saboda Neman Cire Tallafin Fetur' Inji Tsohon Minista
- Tsohon Ministan Harkokin Man Fetur, Dr Ibe Kachikwu, ya fadi matsayar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari kan cire tallafi
- Ya ce 'yan Najeriya sun sha bin dogayen layukan mai, amma ana mika man da aka saya da tallafin gwamnati wasu kasashe
- Ibe Kachikwu ya ce da kyar aka shawo kan Shugaba Buhari, har ya amince da cire tallafin man fetur tare da gindaya sharadi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Tsohon Ministan Harkokin Man Fetur, Dr Ibe Kachikwu, ya bayyana yadda tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya tirje kan ciee tallafin man fetur.
Dr. Kachikwu ya ce Marigayi Buhari, ya ce zai sallame shi idan ƙoƙarin da yake yi na cire tallafin fetur ya ci tura ko ya kara jefa talaka a wahala.

Kara karanta wannan
'Talauci ya yi muni a Najeriya,' El Rufa'i ya ce akwai mafita kan matsin tattalin arziki

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa Kachikwu, wanda ya kasance Ministan Harkokin Man Fetur daga 2016 zuwa 2019, ya ce Buhari yana son talaka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matsalar man fetur ta damu gwamnatin Buhari
Jaridar Leadership ta wallafa cewa Ibe Kachikwu ya ce matsalar dogayen layuka a gidajen mai ta hana shi barci a 2015.
Ya ƙara da cewa a lokacin, sun gano cewa, mafi yawan man da ake shigo da shi cikin Najeriya da tallafin gwamnati, wasu 'yan kasuwa na kara fitar da su zuwa wasu kasashe.
Ya ce:
“Matsala mafi girma da na fara fuskanta lokacin da na zama GMD ita ce layin mai. ’Yan Najeriya kalilan ne ke fahimtar irin wahalar da wannan ke jefa minista ko GMD mai kishin ƙasa ciki."

Source: Getty Images
Ya ce bincikensa ya gano cewa ana fitar da mai zuwa makwabtan ƙasashen bayan an sayo shi da tallafin gwamnati.
Ya ce duk da haɗin gwiwarsa da Kwastam da sauran hukumomi, ba a samu nasarar shawo kan matsalar ba saboda rashin ikon rufe iyakokin ƙasar.

Kara karanta wannan
'Za a yi kwanaki 5 ana malala ruwa,' Gwamnati ta jero jihohi 14 da za su gamu da ambaliya
Gwamnatin Buhari: Yadda aka cire tallafin man fetur
Kachikwu ya bayyana cewa ya sha zuwa wajen Shugaba Buhari yana roƙonsa da a duba yiwuwar sauya farashin fetur domin rage asarar da gwamnati ke yi.
Ya ce:
“Na je wurin shugaban ƙasa sau da dama, na ce masa dole ne mu ƙara farashi. Amma ya ƙi, yana da ra’ayin kare talaka. Daga ƙarshe ya ce: to, yi abin da ka ga dama. Idan ya yi aiki, ba matsala, shikenan. Idan ka gaza, zan sallame ka."
"Na karɓa, na ɗauki kasada, kuma ya yi aiki."
Ya ƙara da cewa ya ƙirƙiri sabon tsarin daidaita farashin mai bisa yadda farashin kasuwannin duniya ya ke.
Tsohon Ministan ya ce wannan ya sa aka cire tallafin fetur gaba ɗaya cikin sauƙi, kuma a cikin awa 48, dogayen layukan mai suka bace a Najeriya.
Ya ce:
“Wannan gyara kaɗan da muka yi, shi ne ya cire tallafin. Ba a sake fuskantar layi ba har zuwa lokacin da na bar ofis. Wannan ya ba ni damar samun barci, kuma gwamnati ta fara samun kuɗi"
Kachikwu ya ce ya ƙi biyan tsoffin basussukan tallafin mai na biliyoyin Naira da ya gada saboda bai amince da sahihancinsu ba.
Tinubu ya fadi amfani cire tallafin fetur
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa matakin da gwamnatinsa ta ɗauka na cire tallafin man fetur zai taimaki jama'a.
Ya nanata cewa daukar matakin ya zama tilas idan ana son tattalin arzikin Najeriya ya shiga taitayinsa tare da taimakon talakan kasa wajen rayuwar yau da gobe.
A cewar Shugaba Tinubu, cire tallafin fetur ya zama wajibi domin an same shi maimakon taimaka wa talakawa, sai ya zama hanyar da ke jefa su cikin ƙarin wahala.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
