Abu 1 tak ne zai kawo karshen matsalar man fetur a Najeriya - Ibe Kachikwu

Abu 1 tak ne zai kawo karshen matsalar man fetur a Najeriya - Ibe Kachikwu

- Abu 1 tak ne zai kawo karshen matsalar man fetur a Najeriya - Ibe Kachikwu

- Yace sai an gyara matatun man fetur na kasa ba cikin hanzari

- Ana zargin dillalan man suma da laifin boye man fetur don samun kazamar riba

Ministan kasa na ma'aikatar man fetur Dr. Ibe Kachikwu ya bayyana cewa Najeriya zata dade tana fama da karancin man fetur muddin ba a gyara matatun man fetur na kasa ba cikin hanzari tare da ba 'yan kasuwa damar gina sabbi domin a bar kasuwa tayi halinta.

Abu 1 tak ne zai kawo karshen matsalar man fetur a Najeriya - Ibe Kachikwu
Abu 1 tak ne zai kawo karshen matsalar man fetur a Najeriya - Ibe Kachikwu

KU KARANTA: Za'a gina sabuwar matatar mai a Arewa

Batun shigo da taceccen mai shine yake jawo matsala, inji Dr. Kachikwu. A yanzu gwamnati kadai ce take shigo da taceccen mai, lamarin da ministan ke gani bai dace ba.

Legit.ng ta samu kuma cewa ana zargin dillalan man suma da laifin boye man fetur don samun kazamar riba.

Aminu Abdulkadir shugaban kwamitin amintattu na kungiyar dillalan man fetur ta kasa yace tsakanin watan Nuwamba da Disamba basu kawo man da suke shigo da shi ba saboda tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya, lamarin da ya kawo rata a tsakanin farashin da suke sayar da mai din a cikin gida da farashin da suka sayowa.

A wani labarin kuma, Sahihan bayanan da muke samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa rukunin kamfanonin nan mallakin gwamnatin tarayya dake kula da albarkatun man fetur watau Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) sun shiga yarjejeniya da gwamnatin jihar Kogi da zummar kafa matatar mai ta zamani watau biofuel plant a turance.

Kamar yadda muka samu, tuni har an kammala saka hannu akan takardar yarjejeniyar a garin Abuja, jiya Talata inda ake sa ran matatar man zata rika samar da mai domin ababen hawa nan ba da dadewa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng