Tura Ta Kai Bango: Likitoci Sun Shiga Yajin Aiki, Sun Gindaya wa Gwamnati Sharuda
- Marasa lafiya, musamman a asibitoci 14 da ke a babban birnin tarayya Abuja, za su shiga garari, yayin da likitoci suka janye aiki
- A ranar Litinin, 8 ga Satumba, 2025, likitoci masu neman kwarewar aiki (ARD) suka sanar da tsunduma yajin aikin gargadi a Abuja
- Likitocin sun gargadi gwamnatin tarayya cewa idan ba a biya bukatunsu ba zuwa makon gobe, za su zarce yajin aikin sai baba-ta-gani
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki reshen Abuja (ARD-FCT) ta tsunduma yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki bakwai.
Likitocin sun janye ayyukansu a asibitocin birnin don nuna bacin ransu kan yadda gwamnatin tarayya ta ke nuna halin ko in kula ga buƙatunsu.

Source: Twitter
Shugaban kungiyar, Dr. George Ebong, ya sanar da shigarsu yajin aikin a yayin zantawarsa da manema labarai a Abuja, in ji rahoton Arise News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin likitoci na shiga yajin aiki a Abuja
Dr. George Ebong ya bayyana cewa matakin shiga yajin aikin ya biyo bayan ƙudurin da aka cimma a taron gaggawa da kungiyar ta gudanar a ranar Juma'a, 5 ga Satumba.
Ya ce duk da tattaunawa mai tsawo da aka yi da hukumomin Abuja, gwamnati ta kasa magance matsalolin da likitoci ke fama da su.
Shugaban ARD-FCT ya kara da cewa tun daga shekarar 2011 ba a kara daukar ma’aikata ba, lamarin da ya jefa likitoci cikin matsin lamba.
Ya kuma ce aiki ba hutu da matsalolin rashin kayan aiki na haddasa illoli masu tsanani, inda aka ruwaito mutuwar wani likita a Port Harcourt saboda irin wannan matsin lamba.
Kungiyar ta kuma yi zargin cewa akwai albashin da aka dakatar da ba su ba tare da wani bayani ba, da kuma uwa uba, zabtare masu kudi da ake yi.
Likitoci sun gargadi gwamnatin tarayya
Dr. Ebong ya ce:
“Mun gaji da irin wannan rikon sakainar kashi da ake yi mana. Muna bukatar a ayyana dokar ta baci a kan asibitocin Abuja, musamman 14 da ake da su kananan hukumomi da yankunan birnin.”
Ya kara da cewa wani malamin jinya ya mutu sakamakon cizon maciji a Asibitin Abaji, al’amarin da ke kara nuna mummunar yanayin aiki da suke fuskanta.
Ya kuma yi gargadi cewa idan gwamnati ta kasa magance matsalolin cikin kwana bakwai, likitocin za su shiga yajin aikin sai baba-ta-gani.

Source: Twitter
Matsayin gwamnati kan yajin aikin likitoci
A gefe guda, Channels TV ta rahoto karamin ministan lafiya, Dr Iziaq Salako, ya bayyana cewa gwamnati na ci gaba da tattaunawa da kungiyar likitocin.
Ya ce babban abin da ke ci gaba da kawo cikas shi ne biyan alawus na zaman likitoci a asibiti, inda har yanzu ba a biya su 40% na shekarar 2025 ba.
“Mun fara tattaunawa da NARD tun farkon mako, kuma muna ganin ana samun ci gaba. Abin da nake fata shi ne mu cimma matsaya kafin wa’adin ya kare."
- Dr Iziaq Salako.
Likitoci sun shiga yajin aiki a LAUTECH
A wani labarin, mun ruwaito cewa, likitoci masu neman kwarewar aiki (ARD) sun tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani a asibitin LAUTECH, da ke Ogbomoso, jihar Oyo.
Likitocin sun ɗauki wannan mataki ne sakamakon gazawar shugabancin asibitin da kuma gwamnatin jihar wajen magance korafe-korafen da suka dade suna yi.
Sun nemi gwamnatin Oyo da hukumar asibitin su biya bukatun su da suka hada da, aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi da biyan bashin albashin da ya fara daga Janairun 2025.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


