'Yan Bindiga Sun Kutsa Gidan Shugaban Jam'iyyar APC, Sun Sace Matarsa da 'Yarsa

'Yan Bindiga Sun Kutsa Gidan Shugaban Jam'iyyar APC, Sun Sace Matarsa da 'Yarsa

  • 'Yan bindiga sun kai hari gidan shugaban jam'iyyar APC, Alhaji Muhammad Swasun, inda suka yi awon gaba da matarsa da ’yarsa
  • An ce miyagun sun yi barin wuta a cikin garin Patigi, jihar Kwara, lamarin da ya tsoratar jama'a, yayin da suka tsere da matan biyu
  • Kwamishinan ’yan sandan jihar Kwara, Adekimi Ojo, ya yi bayani game da harin da 'yan bindigar suka kai gidan shugaban APC

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara – Hankula sun sake tashi a jihar Kwara, yayin da wasu ’yan bindiga suka farmaki gidan shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Patigi, Alhaji Muhammad Swasun.

Maharani sun yi awon gaba da matar shugaban jam’iyyar, Hajiya Fatima, tare da ’yarsu Amina, a daren Lahadi, da daddare.

'Yan bindiga sun shiga har cikin gida, sun sace mata da 'yar shugaban jam'iyyar APC a Kwara.
Gungun magoya bayan APC a wani gangamin jam'iyyar da aka gudanar a jihar Imo a Fabrairun 2023. Hoto: @GoziconC
Source: Twitter

'Yan bindiga sun farmaki gidan shugaban APC

Kara karanta wannan

'Abubuwa 4 ne ke rura wutar ta'addanci,' Gwamna Uba Sani ya nemo mafita ga Arewa

Lamarin ya faru ne a yankin Sakpefu, inda maharan suka shigo cikin gidan bayan tsallaka katanga, sannan suka yi ta harba bindiga a sama, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani rahoto ya nuna cewa ’yan bindigar sun shafe mintoci da dama suna harbe harbe kafin su shiga cikin dakunan gidan.

'Yan bindigar sun tarar da matar shugaban jam’iyyar tare da ’yarsa a cikin dakin, inda suka yi awon gaba da su zuwa cikin jeji.

Wani jigon jam’iyyar APC a jihar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata hira da manema labarai a safiyar Litinin.,

A cewar jigon:

"Gaskiya ne cewa an sace matar shugabanmu da 'yarsa a Patigi a daren jiya. Na yi magana da shi a safiyar yau, ya ce ya auna arziki ne kawai, shi ma da 'yan bindigar sun tafi da shi."

'Yan bindiga sun sace iyalan shugaban APC

Pulse.ng ta tattaro cewa ‘yan bindigar sun dauki tsawon mintuna kafin su tafi da waɗanda suka sace zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna a Katsina, an samu asarar rayuka

Wani ganau ya ce:

"Maharan sun sace matarsa, Haja Fatima, da 'yarsa, Amina, kuma suka tafi da su zuwa wani wuri da ba a sani ba."

Wasu shaidun gani da ido sun ce ’yan bindigar sun yi ta harbe-harbe a cikin garin don tsoratar da al’umma kafin tsere wa da wadanda suka sace.

An ce sun yi ta barin wuta a saman iska lamarin da ya tilasta mutane neman mafaka cikin tsoro, yayin da su kuma suka sulale.

'Yan bindiga sun yi awon gaba da iyalan shugaban jam'iyyar APC a jihar Kwara
Taswirar jihar Kwara. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Martanin 'yan sanda kan harin Kwara

Garin Patigi da wasu sassan Kwara ta Arewa sun dade suna fama da matsalar masu garkuwa da mutane.

Mutane a yankin na ta kira gwamnati da jami’an tsaro da su dauki mataki mai karfi wajen kawo karshen lamarin.

Da aka tuntubi kwamishinan ’yan sandan jihar Kwara, Mista Adekimi Ojo, ya ce har yanzu bai samu rahoton garkuwa da iyalan shugaban jam'iyyar ba tukuna.

“Har yanzu ban samu cikakken bayani kan wannan lamari daga jami’aina ba tukuna.”

Kara karanta wannan

Ta fara tsami tsakanin gwamna da ministan tsaro, APC ta fusata kan lamarin

- CP Mista Adekimi Ojo.

'Yan bindiga sun sace shugaban APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ƴan bindiga sun sace shugaban APC na mazaɓa ta 5 a ƙaramar hukumar Ose da ke jihar Ondo.

Wata majiya ta bayyana cewa masu garkuwar sun lakaɗa wa shugaban jam'iyyar dukan tsiya kafin su tasa keyarsa zuwa cikin daji.

Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Ondo, mafarauta da sojoji sun bazama cikin jeji domin ceto wanda aka sace, tare da kama miyagun.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com