Mataimakin Gwamnan Kano Ya Gana da Sheikh Jingir kan Rasuwar Malamin Izala
- Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Jihar Filato inda ya gudanar da taruka da dama
- Gwarzo ya ziyarci Sheikh Sani Yahaya Jingir domin yin ta’aziyya bisa rasuwar ɗan uwansa a watannin baya tare da yin addu’a ga mamacin
- Haka kuma ya kaddamar da ofishin Kwankwasiyya a Jos, ya gana da shugabannin jam’iyya da kungiyoyi daban-daban, ya halarci bikin yaye dalibai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato – Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya gudanar da ziyarar aiki ta musamman a Jos, Jihar Filato.
Ziyarar ta haɗa da tarurruka, ziyartar shugabanni, kaddamar da ayyuka, da kuma halartar bikin yaye dalibai.

Source: Twitter
Legit ta tattaro bayanai kan ziyarar mataimakin gwamnan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwarzo ya yi amfani da wannan dama wajen jaddada zumuncin tarihi da ke tsakanin Kano da Filato, musamman a fannoni na kasuwanci, ilimi da al’adu.
A lokacin ziyarar tasa, ya kuma halarci wuraren siyasa da zamantakewa, tare da bayyana cewa mutuncin al’umma da haɗin kan jihohin biyu na da muhimmanci ga dorewar ci gaban kasa.
Aminu Gwarzo ya ziyarci Sheikh Jingir a Filato
Gwarzo ya kai ziyara ta musamman ta ta’aziyya ga Sheikh Sani Yahaya Jingir, bisa rasuwar ɗan uwansa, marigayi Sa’idu Hassan Jingir.
Ya yi addu’ar neman rahamar Allah ga mamacin tare da bayar da hakuri ga iyalansa da wadanda rashin ya shafa.
Mataimakin gwamnan ya jaddada muhimmancin yin juriya da dogaro ga Allah a irin wannan lokaci na rashi.
Ganawar Aminu Gwarzo da gwamnatin Filato
Bayan haka, mataimakin gwamnan ya kai ziyara ta ban girma ga mataimakiyar gwamnan Jihar Filato, Hajiya Josephine Piyo.
Rahoton Prime Time News ya nuna cewa ya bayyana manufar ziyara, tare da nuna godiya bisa kyakkyawar tarbar da gwamnatin jihar ta yi masa.
Ya tuna yadda ya gudanar da hidimar kasa (NYSC) a Filato shekaru 37 da suka gabata, yana mai bayyana jihar a matsayin wuri mai ɗimbin tarihi da natsuwa.

Source: Twitter
A nata jawabin, Josephine Piyo ta bayyana Filato a matsayin daya daga cikin jihohin da suka fi kyau a Najeriya, tana mai kira ga ci gaba da zumunci da haɗin kai tsakanin Kano da Filato.
Tattaunawa da shugabannin NNPP na Filato
Haka kuma Gwarzo ya gudanar da taron duba tsare-tsare tare da shugabannin jam’iyyar NNPP da Kwankwasiyya a jihar, karkashin jagorancin Hon. Abdurrahmani Mai Kadama.
Rahotanni sun nuna cewa sun tattauna kan dabarun ci gaba da karfafa jam’iyya da tabbatar da zaman lafiya a Filato.
Baya ga haka, Gwarzo ya kaddamar da sabon ofishin Kwankwasiyya a karamar hukumar Jos ta Arewa.
Abba ya taya Sanusi II murnar gama PhD
A wani rahoton, kun ji cewa Abba Kabir Yusuf ya taya mai martaba Muhammadu Sanusi II murnar gama digirin PhD.
A makon da ya wuce ne aka yi taron kammala karatun da Sarkin ya yi a birnin London na Birtaniya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa za su yi hadaka da jami'ar London domin karfafa jami'ar North West da ke Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
