Najeriya, Ƙasashe 9 Za Su Fuskanci Kusufin Wata, an Ji Tsawon Lokacin da Zai Dauka
- Rahotanni sun tabbatar da cewa Najeriya za ta fuskanci kusufin wata a yau Lahadi 7 ga watan Satumbar 2025
- An tabbatar da cewa Najeriya da wasu ƙasashe za su shaida kusufin wata a yau Lahadi wanda zai ɗauki fiye da awa 1
- Masana sun ce za a iya hango kusufin a yawancin Afirka ciki har da Najeriya, Ghana, Kamaru, Binin, Togo, Chadi da sauransu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Masana kimiyya sun yi bincike inda suka gano a yau za a samu kusufin wata a Najeriya da wasu kasashe da ke Afirka.
An ce Najeriya da ƙasashe akalla tara a Nahiyar Afrika za su fuskanci kusufin wata a yau Lahadi 7 ga watan Satumbar 2025.

Source: Getty Images
Za a fuskanci kusufin wata a Najeriya
Rahoton NTA News ya tabbatar da lamarin inda ya ce ana sa ran faruwar hakan da daren yau Lahadi a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun shaida kusufin watan zai faru da misalin karfe 8:00 na daren ranar Lahadi, 7 ga Satumba, wanda zai ɗauki kusan mintuna 83.
Masana sun kuma bayyana cewa za a iya hango shi a yawancin kasashen Nahiyar Afirka da bakaken fata suka fi yawa.
Kasashe da suka haɗa da Najeriya, Ghana, Kamaru, Gabon, Nijar, Chadi, Binin, Togo, da São Tomé za su shaida kusufin.
Har ila yau, masana sun ce ba kamar rana ba, kallon kusufin wata da ido kai tsaye ba ya da wata illa ko haɗari ga lafiyar ido.

Source: Getty Images
Me yake kawo kusufin wata?
Cikakken kusufin wata na faruwa ne idan rana, duniya da wata suka hadu a layi ɗaya, duniya ta shiga tsakani ta rufe hasken rana.
Hakan yake sa inuwar Duniya ta sauka kan Wata, ta kan jawo duhu tare da mayar da shi launin ja, rahoton Punch ya tabbatar.
Lamarin ya jawo hankalin masu kallo da masana kimiyya, inda ya zama babban lamari na lura da sararin samaniya a faɗin Afirka.
Hukumar NASA ta yi karin haske
Hukumar kula da sararin samaniya NASA ta bayyana cewa ana samun kusufin wata iri-iri; cikakke, rabinsa, ko kuma akasin haka.
Hukumar ta yi hasashen cewa za a ga cikakken kusufi a Turai, Afirka, Asiya da kuma Ostiraliya a ranar Lahadi.
Bayyanar ja-ja a jikin Wata, wadda ake kira “blood moon,” na faruwa ne sakamakon hasken rana da ke ratsa yanayin Duniya.
Sabanin kusufin rana da ke bukatar kariya ta musamman a ido, wannan kusufin wata ba ya da hatsari ga ido kai tsaye.
An sanar da samun kusufin rana a Najeriya
A baya, mun ba ku labarin cewa rana ta yi kusufi a ranar Alhamis 1 ga watan Satumbar shekarar 2016 wanda ya jefa mutane cikin firgici.
An tabbatar da hakan ya faru ne da hantsi a wasu yankunan Najeiriya kamar yadda hukumomi suka tabbatar a kasar.
Hukumar binciken sararin samaniya, NASRADA ce ta sanar da haka kafin faruwar lamarin. ta sanar da cewa, rana za ta yi kusufi a kasar.
Asali: Legit.ng

