Allah mai iko: Za a gamu da husufin wata yau a Najeriya
- Yau rana za ta kama wata na fiye na awa guda a wasu bangarorin Duniya
- Wannan ne zai zama husufin da ya fi kowane dadewa a wannan karnin
Mun samu labari cewa manyan Masana harkar taurari da yanayi sun bayyana cewa za a gamu da husufin wata yau. Farfesa Augustine Ubachukwu ya bayyanawa ‘Yan Jarida wannan a Garin Abuja.
Augustine Ubachukwu wanda Malami ne a Jami’ar Najeriya ta Nsulla ya bayyana cewa za a ga rana ta kama wata a cikin daren nan. Masanin yace wannan abu zai faru ne tsakanin karfe 9:30 zuwa kusan 11:22 na daren yau dinnan.
KU KARANTA:
A bayanin da yayi wa manema labarai, babban Farfesan ya bayyana cewa husufin watan zai dauki lokaci kimanin sa’a guda a Najeriya. Wannan abu dai ba a Najeriya kurum zai faru ba domin zai shafi har Nahiyar Amurka ta Kudu.
Za a fi ganin bayyanar husufin ne a Nahiyar Turai da kuma Kasashen Ustaraliya da kuma Yankin Asiya da Kasar New Zealand da kuma nan Afrika. An dai fi shekara 100 ba a taba samun husufin da zai dauki kusan awa guda ba a Duniya.
A kan samu kusufin ne idan har rana ta kama wata a cikin daren da wata ya cika. Kasar New Zealand ce za ta fara ganin wannan abin mamaki jim kadan bayan faduwar rana inji Masanan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng