Hotunan yadda aka yi Khusufin rana a fadin duniya

Hotunan yadda aka yi Khusufin rana a fadin duniya

- A ranar Lahadi ne aka samu 'zazzabin' rana a wasu bangarorin duniya da suka hada da Yammacin Afrika, Kudancin Asia, Kudancin China da kasar Taiwan

- Khusufi na rana na faruwa ne idan wata ya ratsa tsakanin rana da duniya, lamarin da ke kawo disashewar hasken ranar

- A kan samu khusufi sau daya ko sau biyu a shekara a fadin duniya, amma ba kowanne sassan duniyar ne ke gane faruwar hakan ba

Masu kallo daga wasu bangarorin duniya da suka hada da Yammacin Afrika, Larabawa, Kudancin Asia, Kudancin China da kasar Taiwan sun bayyana cewa rana ta yi zazzabi a wani yanayi mai matukar bada mamaki.

Masu daukar hoto daga sassan duniya sun dauka hotunan khusufin ranar.

Khusufi dai kalmar larabci ce amma bahaushe na kiranta da 'zazzabi'. Khusufi ko zazzabin rana na faruwa ne idan wata ya ratsa ta tsakanin duniya da rana. Hakan na kawo disashewar hasken ranar mai yawa ko kuma kadan.

Khusufin ko kuma mu ce zazzabin ranar ya faru ne a ranar tsakiyar bazara. A kan kirata da rana mafi tsayi ga jama'ar da ke zama a arewacin kusurwar duniya.

Rana kan yi zazzabi sau daya ko biyu a shekara kuma ana iya ganin hakan a wani sassa na bangarorin duniya.

Zazzabin rana baya wuce dakika 90, hakan ne kuwa ake kira da kololuwarsa.

Jama'a da dama ba su ga yadda ranar ta yi khusufi ba saboda nisan daruruwan kilomita da suke da ita daga tsakiyar kusurwar.

Amma kuma da yawa an ga alamu da ke nuna khusufin ranar.

Masana ilimin taurari sun tabbatar da cewa ana iya kamanta khusufin ranar da sauya kalar kwan wutar lantarki daga karfin 500W zuwa karfin 30W.

Ga kadan daga cikin hotunan yadda khusufin ya bayyana a wasu kasashen duniya da suka gan shi kiri-kiri.

Hotunan yadda aka yi Khusufin rana a fadin duniya
Karachi, Pakistan. Hoto daga BBC
Asali: Twitter

Hotunan yadda aka yi Khusufin rana a fadin duniya
Mumbai, India. Hoto daga BBC
Asali: Twitter

KU KARANTA: Harbi a Aso Rock: An sauya wa dogarai 20 na Buhari wurin aiki

Hotunan yadda aka yi Khusufin rana a fadin duniya
Chiayi, Taiwan. Hoto daga BBC
Asali: Twitter

Hotunan yadda aka yi Khusufin rana a fadin duniya
Manila, Phillipines. Hoto daga BBC
Asali: Twitter

Hotunan yadda aka yi Khusufin rana a fadin duniya
Guangzhou, China. Hoto daga BBC
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel