Rana za ta yi khusufi a Nigeria a farkon watan gobe
-Rana za ta yi khussufi a ranar Alhamis 1 ga watan Satumba
-A na sa ran hakan zai faru ne da hantsi
-Hukumar binciken sararin samaniya ce ta sanar da hakan
Hukuma mai bincike a sararin samaniya ta Najeria NASRADA, a jiya 16 ga watan Agusta ta sanar da cewa, rana za ta yi khusufi a kasar.
A wata sanarwa da Hukumar ta fitar ta ce, Khusufin wanda ta ce za a iya ganinsa a ko ina a kasar, zai faru ne daga misalin karfe 7:15 zuwa 10:03 na ranar Alhamis din sabon wata mai kamawa na Satumba.
Sanarwar wacce Dakta Felix Ale, shugaban hulda da ‘yan jaridu na Hukumar ya sa wa hannu ta ce, bacewar rana zai iya zama gaba daya, ko kuma rabi da rabi a wasu wuraren cikin kasar, a yayin da a kudancin kasar, musamman a Lagos, ranar za ta buya da kimanin kashi 80.
KU KARANTA:Bitar wasu muhimman labarun Legit.ng na ranar Talata
Garuruwan arewacin kasar kamar Sokoto ranar za ta kasance kimanin kashin 45 ne zai buya, haka ma babban birnin tarayyar Abuja, ranar za ta buya ne da kimanin kashi 60, sauran garuruwa abin zai fi haka, a cewar sanarwar.
Dakata Ale a cikin sanarwar ya ci gaba da cewa, kar jama’a su firgita da afkuwar khusufin, domin wani abu ne na kimiyya, wanda bincike ka iya hasashen faruwarsa, kuma Hukumar NASRADA ta samu nasarar yin hakan ne a bisa dokar da ta kafata.
Sanarwar ta yi gargadin kallon rana da ido kai tsaye ba tare da tare gilashi na musamman ba, wanda hakan na iya lahanta idanu, har ya kai ga makanta.
Asali: Legit.ng