Gwamna Ya Fito Ya Fadi Gaskiya, Ya Ce An Kashe Jami'an Tsaro Sama da 76
- Gwamnan Benuwai ya tabbatar da cewa akalla jami'an tsaro 76 ne suka rasa rayukansu a yaki da matsalar tsaron jihar
- Rabaran Hyacinth Alia ya ce gwamnatinsa za ta taimaki matansu kuma za ta dauki nauyin karatu tare da kulawa da 'ya'yansu
- Gwamnan jihar ya kuma bai wa iyalan kowane jami'i da aka kashe a bakin aiki a Benuwai kyautar Naira miliyan biyar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Benue - Gwamnan Benuwai, Rabaran Hyacinth Alia, ya bayyana cewa akalla jami’an tsaro 76 sun rasa rayukansu a kokarin kare jama'a cikin shekara guda a jihar.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi bakuncin iyalan jami'an tsaron da aka kashe a Makurdi, inda ya tabbatar musu cewa sadaukarwarsu ba za ta tafi a banza ba.

Source: Facebook
Vanguard ta rahoto cewa Gwamna Alia ya baiwa kowane iyali daga cikin waɗanda suka rasa ransu Naira miliyan biyar (N5m) domin tallafa masu.

Kara karanta wannan
Kalaman Gwamna Dauda kan ta'addanci sun jaza masa, an 'gano' maƙarƙashiya da yake yi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kashe sojoji, 'yan sanda da wasu a Benuwai
Jami'an da suka rasa rayukansu a bakin aiki saboda matsalar tsaro a Benuwai sun hada da na ‘Yan Sanda, NSCDC, Sojoji, Benue State Civil Protection Guards da dakarun Operation Zenda.
Gwamnan ya yaba da jajircewa da sadaukarwar jami'an tsaron, yana mai cewa sun bayar da rayukansu domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Ya kuma gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Babban Hafsan Tsaro da sauran shugabannin rundunonin tsaro bisa irin ƙoƙarin da suke yi wajen dawo da zaman lafiya a Benuwai.
Gwamna zai kula iyalan jami'an da aka kashe
A rahoton Leadership, Gwamna Alia ya ce:
“Wannan babban rashi ne gare mu, amma za mu ci gaba da tafiya tare da ku. Zamu tabbatar da cewa ‘ya’yanku ba su daina karatu ba ta hanyar daukar nauyinsu.
"Za mu ci gaba da ziyartarku lokaci zuwa lokaci. Ba za mu bari a bar kowa a baya ba. Za ku kasance a jerin waɗanda gwamnati ke kula da su kai tsaye.
"Ina tabbatar muku da cewa jinin 'yan uwanku da aka zubar ba zai tafi a banza ba, dole zaman lafiya ya dawo a jihar Benuwai.”

Source: Facebook
Gwamna Alia ya godewa matar Tinubu
Gwamna Alia ya kara da cewa gwamnatinsa za ta tallafawa matan jami'an tsaron da suka rasa rayukansu, sannan za a kula da yaran da ba su san iyayensu da iliminsu.
Haka kuma ya gode wa uwargidar shugaban kasa da ƙungiyar tallafawa yan gudun hijira ta kasa da kasa (IOM) bisa tallafin da suke ba wa mutanen da suka rasa matsugunansu.
'Yan bindiga sun kashe mutane a Benuwai
A wani rahoton, kun ji cewa ‘yan bindiga sun kashe mutane biyu tare da jikkata wani mutum guda a yankin karamar hukumar Ogbadibo ta jihar Benuwai.
Bayanan da aka samu sun nuna cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 1:55 na tsakar dare lokacin da wasu ‘yan bindiga da ba a tantance adadinsu ba suka mamaye kauyen Ejema.
Majiyoyi sun ce bayan aukuwar harin, jami’an ‘yan sanda ƙarƙashin DPO na Orokam, tare da haɗin gwiwar wata tawagar tsaro, sun shiga aikin sintiri da kai dauki a yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
