Albarkacin Shettima, An Ƴanta Fursunoni 59, An Ɗauki Nauyin Karatun Marayu a Bauchi
- Kungiyar matasan APC, a Arewa maso Gabas ta ’yanta fursunoni 59 domin murnar cikar Kashim Shettima shekaru 59 da haihuwa
- Baya ga haka, kungiyar ta ba da kyautar magungunan N1m ga gidan yarin Bauchi, sannan ta dauki nauyin karatun marayu 59
- Shugaban kungiyar, Kabiru Garba Kobi, ya ce bayyana dalilin da ya sa suke gudanar da ayyukan alheri a madadin Shettima
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi - Wata kungiyar matasan jam’iyyar APC, a Arewa maso Gabas (APC-YPNE), ta ’yanta fursunoni 59 daga gidan yarin Bauchi a ranar Juma’a, 5 ga Satumba, 2025.
Shugaban kungiyar, Kabiru Garba Kobi, ya ce sun 'yantar da fursunonin domin murnar cikar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, shekaru 59 da haihuwa.

Source: Facebook
Kashim Shettima: Kungiya ta 'yanta fursunoni 59

Kara karanta wannan
Likitoci sun yi tsayin daka kan tafiya yajin aiki, sun fadi yadda gwamnati ke muzguna masu
Kabiru Garba Kobi, ya shaida wa Legit Hausa cewa sun nemi jerin sunayen fursunonin da ke da kananan laifuffuka, inda suka biya kudaden tara domin a sakesu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baya ga 'yanta fursunoni, kungiyar ta kuma mika magunguna da darajarsu ta kai Naira miliyan ɗaya ga gidan yarin Bauchi, domin kula da lafiyar fursunonin da ke fama da rashin lafiya.
Shugaban kungiyar ya ce wannan wani yunkuri ne na rage cunkoso a gidajen yari da kuma tallafa wa kokarin gwamnati na inganta walwalar fursunoni.
Daga cikin fursunoni 59 da aka 'yantar akwai, Yusuf Amadu, Dahiru Musa, Nasir Alhasan, Sani Ahmad, Y Bala, Garba Makeri, Salim Sani, da dai sauransu.
Kungiyar APC ta dauki nauyin marayu 59
A wani taro na musamman da kungiyar ta gudanar a otal din Distination Bauchi, matasan sun sanar da daukar nauyin karatun marayu 59.
Kabiru Kobi ya bayyana cewa marayun za su samu ingantaccen karatun firamare wanda zai share masu fagen shiga sakandare da manyan makarantu.
Kungiyar ta kuma raba tallafin kuɗi, magunguna da kayayyakin more rayuwa ga marayun, duk don murnar zagayowar ranar haihuwar Shettima.
Ayyukan matasan APC a madadin Shettima
Kabiru Garba Kobi ya ce dukkan ayyukan da suka gudanar kauna ce kawai, ba tare da wata alaƙa ta kai tsaye da ofishin mataimakin shugaban kasa ba.
Da yake karin haske kan dalilin yin wadannan ayyuka, Kabiru Kobi ya ce:
“Mun ’yantar da fursunoni 59, kuma mun dauki nauyin karatun marayu 59, domin murnar cikar Kashim Shettima shekaru 59 da haihuwa.
"Mun zabi yin abin da zai sanya farin ciki a zukatan al’umma maimakon yin gurasar murnar haihuwa.
“Ina so mutane su sani cewa wannan kungiya tana gudanar da ayyukanta ne a kashin kanta, ba tare da zuwa wajen mataimakin shugaban kasa ba. Kauna ce kawai ta sa muke yin komai a madadinsa.”

Source: Twitter
Matasa sun jaddada goyon baya ga Shettima
Kungiyar matasan na APC ta aika da sako kai tsaye ga Shettima, inda Kabiru Garba Kobi ya ce:
“Muna masa fatan alheri, kuma muna jaddada goyon baya gare shi. Muna gaya masa cewa ya yi hakuri da mutanen banza, dama Sardauna ya ce: 'Ba ka iya wa, ba ka gamawa, kuma ba a yaba ma'. Amma mu abin da muka yi imani da shi shi ne, yana kan daidai, kuma yana kokari.”
Game da kira da wasu ke yi na a sauya Shettima matsayin abokin takarar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027, Kabiru Kobi ya ce:
“Mu abin da ya sa muke son Shettima shi ne, yana da wani irin Tauhidi da ba kowane ya ba shi ba. Shi ya dogara da Allah, shi ya sa duk 'yan soki-burutsun siyasa, ba su taba samun nasara a kansa ba.”
Ya kara da cewa ba za su yi shiru ba yayin da ake yada maganganu marasa dadi kan Shettima. Maimakon fada da kalamai, za su ci gaba da yin ayyukan alheri a madadinsa.
Kalli hotunan taron a nan kasa:
Shettima: APC ta yi martani ga kalaman Babachir
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar matasan APC, a Arewa maso Gabas (APC-YPNE) ta soki Babachir Lawal saboda kalamansa kan Kashim Shettima.
Shugaban kungiyar, Kabiru Garba Kobi ya zargi Babachir da raina Shettima tare da nuna kiyayyarsa a fili kan tikitin Musulmi da Musulmi da aka yi a 2023.
Kabir Garba Kobi ya shaidawa Legit Hausa cewa hassada ce kawai ke cin Babachir, kuma yana ji yana gani Shettima zai kara daukaka a gwamnatin APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

