Obasanjo Ya Fasa Kwai, Ya Fallasa Yadda 'Yan Majalisa Ke 'Satar Kudaden Jama'a'

Obasanjo Ya Fasa Kwai, Ya Fallasa Yadda 'Yan Majalisa Ke 'Satar Kudaden Jama'a'

  • Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce ’yan majalisa na yanzu sun fi na baya muni wajen cin hanci da rashawa
  • Obasanjo ya bayyana ayyukan mazaba na 'yan majalisa a matsayin "fashin kudin jama'a da rana tsaka ba tare da makami ba”
  • Ya tuno yadda aka kai ruwa rana kafin aka amince da dokar kafa EFCC, saboda wasu ‘yan majalisar na tsoron zuwa gidan yari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya sake dura kan ’yan majalisar Najeriya, inda ya bayyana su a matsayin mafi muni fiye da na jamhuriyar farko, ta biyu da ta uku.

Ya bayyana cewa ’yan majalisa sun kirkiri tsarin “ayyukan mazabu” domin tara haramttun kudi, abin da ya kira da “sata kiri-kiri a tsakar rana.”

Kara karanta wannan

Minista ya fadi yadda manufofin Tinubu su ka ceto albashin ma'aikata a jihohi 27

Obasanjo ya fallasa yadda 'yan majalisa ke cin hanci da rashawa da take kundin mulkin Najeriya
Olusegun Obasanjo a wani taron kasashen Afrika , da zauren majalisar tarayya da ke Abuja. Hoto: @femigbaja, @Oolusegun_obj
Source: Twitter

Obasanjo ya yi kaca kaca da 'yan majalisa

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, Obasanjo ya bayyana hakan ne a daya daga cikin littattafansa da aka fitar, mai suna 'Najeriya jiya da gobe: Nazari kan tarihin Najeriya da makomarta a nan gaba.'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A babi na bakwai na littafin mai taken "Yan majalisar tarayya da na jihohi,' Obasanjo ya tuna cewa sau biyu ya yi aiki da ‘yan majalisar Najeriya, lokacin yana shugaban soja da kuma shugaban kasa na dimokuradiyya.

A lokutan nan biyu, Obasanjo ya ce bai ga wani abin a zo - a gani a da 'yan majalisar ke yi don gina Najeriya ba, sabanin yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Yadda majalisa ta yi yunkurin hana kafa EFCC

Tsohon shugaban kasar ya ce sai da aka shafe shekara daya da rabi kafin majalisa ta amince da dokar da ta kafa hukumar EFCC, bayan an kai ruwa rana wajen gyara gyarenta.

Kara karanta wannan

Saudi da Faransa za su kawo karshen Isra'ila game da shiga Gaza

A cewarsa, wasu daga cikin 'yan majalisar sun ce idan suka zartar da dokar kamar yadda aka aika musu da ita tun farko, za su iya shiga gidan yari bayan wa'adin mulkinsu.

Obasanjo ya ce dole ya amince da dokar yadda suka kawo masa, saboda an sanar da shi cewa, 'yan majalisar za su yi watsi da dokar idan ya sake mayar masu da ita.

Cif Obasanjo ya zargi 'yan majalisa da rashawa

Obasanjo ya ce mafi munin abin da 'yan majalisa na yanzu suke aikata wa "shine mugun hali na cin hanci da rashawa da kuma take kundin tsarin mulki."

Ya ce kundin tsarin mulki ya baiwa hukumar RMAFC damar tantance albashi da alawus, amma ’yan majalisa sun dauki wannan iko sun dora shi a kansu.

Tsohon shugaban kasa ya ce:

“'Yan majalisar sun yi watsi da tanadin kundin tsarin mulkin, sun ba kawunansu albashi da alawus-alawus mai yawa, inda suka zarce 'yan majalisun kasashe masu tasowa, har ma da wasu da suka ci gaba."

Obasanjo ya bayyana cewa lokacin da yake shugaba, ya ki sakin wasu kudi da majalisar ta ware da gangan domin kashewa kan abubuwan da ba su da amfani, lamarin da ya jawo masa barazanar tsigewa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amsa kira kan kirkirar 'yan sandan jihohi, ya gano sirrin magance ta'addanci

Olusegun Obasanjo ya zargi 'yan majalisar Najeriya da bullo da 'ayyukan mazabu' don wawure kudin jama'a.
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a taron kaddamar da wani littafinsa a Abuja. Hoto: @Oolusegun_obj
Source: Twitter

Obasanjo ya kira ayyukan mazabu da 'sata'

Obasanjo ya zargi ’yan majalisa da ƙirƙirar tsarin ayyukan mazabu domin yashe kudin jama'a ta haramtacciyar hanya, ba tare da amincewar bangaren zartarwa ba.

Ya ce wannan ya lalata tsarin kasafin kudi, ya jefa kasa cikin gibin kudi, sannan ya koma abin dariya.

A cewarsa:

“Ayyukan mazabu a matakin kasa ko jiha sata ce a bainar jama’a. Ya kamata a dauki duk wanda yake da hannu a kwashe kudin jama'a da sunan ayyukan mazabu a matsayin mai laifi.”

Obasanjo ya kara da cewa daga lokacin mulkin Muhammadu Buhari ne kwashe kudi ta hanyar ayyukan mazabu ta yi muni, inda 'yan majalisar ke wawushe kudin a fili ba tare da wata kunya ba.

"A yanzu, babu boye-boye ko wata kunya; suna aikata hakan a fili ba tare da tsoro ba, kuma shugaban kasa ya kasa taka masu burki, don haka shi ma ya zama abokin aikata laifin."

Kara karanta wannan

Ribadu ya karyata El-Rufai, ya zarge shi da siyasantar da matsalar tsaro

- Olusegun Obasanjo.

'Yadda na yi mulki daga 1999-2007' - Obasanjo

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Olusegun Obasanjo ya ce gwamnatinsa na daga cikin mafi nagarta wajen gudanar da mulkin dimokuradiyya a tarihin Najeriya.

Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne yayin da yake bayani kan yadda ya gudanar da mulkin Najeriya daga shekarar 1999 zuwa 2007.

Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ya samu Najeriya da tulin bashi, amma kafin ya sauka sai da ya tabbatar ƙasar ta samu rarar kudi a lalitarta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com