‘Laifi ne’: Za a Hukunta Yan Mata da Ke Saba Alkawari bayan Karbar Kudin Samari
- Rundunar ’yan sanda ta Jihar Rivers ta yi karin haske game da abin da ke faruwa tsakanin yan mata da samari
- Rundunar ta gargadi yan mata da ke karɓar kuɗin mota daga maza ba tare da halartar inda suka shirta haduwa ba
- Kakakin ’yan sanda, Grace Iringe-Koko ita ce ta tabbatar da haka inda ta ce hakan na iya kaiwa ga kamawa da gurfanarwa a kotu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Rundunar yan sanda ta fitar da sanarwa a jihar Rivers game da alaka tsakanin yan mata da samari.
Rundunar ’yan sanda ta gargadi yan mata cewa karɓar kuɗin mota daga saurayi sannan a kasa halartar ganawar na zama babban laifi.

Source: Twitter
Kakakin rundunar, Grace Iringe-Koko, ta bayyana hakan a wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Facebook, inda ta ja hankalin matasa mata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta daure mata bayan cin amanar saurayi
Wannan matsala da mata ke karbar kudin mota ba tare da ziyartar samarinsu ba na ci gaba da zama ruwan dare a Najeriya.
Hakan ne ma ya sa wasu mazan ke kai kara kotu domin bi musu kadunsu bayan cin amanar da matan ke musu.
Ko a watan Janairun 2025, kotu ta ci tarar wata mata N150,000 a jihar Osun bayan karbar kudin mota amma ta sabawa saurayin alkawari, cewar Channels TV.
Hukuncin da ke jiran mata masu cin amana
Grace ta ce babu dalilin da zai sa mace ta karbi kudin mota daga saurayinta kuma ta gaza cika alkawari.
Ta tabbatar da cewa hakan na kawo matsaloli da dama musamman tsakanin masoyan idan har hukuma ba ta shiga tsakaninsu ba.
Ta ce:
“Meya sa za ki karɓi kuɗin mota daga wani namiji ba tare da kin je kika same shi ba? Laifi ne babban da ke bukatar hukunci."

Kara karanta wannan
An tsinci gawa gefen ofishin sakataren gwamnatin Tinubu, majalisa ta yi karin haske

Source: Original
Yan sanda sun gargadi mata kan ziyartar samari
Rundunar ta ƙara da cewa wannan laifi ne kuma wanda aka same shi da laifi na iya fuskantar ɗaurin shekara uku a kurkuku.
Grace ta gargadi mata da su guji almundahanar kuɗi, tana mai jaddada cewa abin da suke ɗauka wasa na iya haifar da mummunan sakamako.
Ta bayyana cewa wanda aka same shi da laifin zai iya fuskantar ɗaurin shekaru uku, tare da kira ga mata su guji almundahana.
Sashe na 419 na dokar laifuffuka ya haramta duk wata hanya ta karɓar kuɗi ko dukiya ta hanyar yaudara, abin da aka fi sani da “damfara.”
Magidanci ya kama matarsa da wani kato
Mun ba ku labarin cewa wani magidanci ɗan shekara 38 a duniya ya ga abin mamakin da bai taɓa tsammani ba lokacin da ya dawo gida ba tare da sanar da matarsa ba.
Mutumin mai suna, Mpanga ya bayyana yadda ya samu matarsa da wani mutumi tsirara a gadon aurensu.
Kotu ta ci tarar kwarton da aka kama maƙudan kuɗi sannan ta yi wa matar nasiha kan ta gujewa cin amana da neman maza.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

