Hukumar EFCC Ta Kafe Hoton Tsohon Kwamishina, Tana Nemansa Ruwa a Jallo

Hukumar EFCC Ta Kafe Hoton Tsohon Kwamishina, Tana Nemansa Ruwa a Jallo

  • EFCC ta ayyana tsohon kwamishinan kananan hukumomi, Christopher Enweremadu, a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo
  • Ana zargin tsohon kwamishinan da hannu a cikin badakalar karkatar da kudade da kuma almundahana a lokacin da yake ofis
  • Wannan na zuwa ne bayan wata kotu da ke birnin tarayya, Abuja, ta bada umarnin binciken kudaden kananan hukumomin jihar Abia

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta ayyana wani Christopher Enweremadu, a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.

Christopher Enweremadu, tsohon kwamishinan kananan hukumomi da masarautu ne na jihar Abia, da ke Kudu maso Gabashin kasar nan.

Hukumar EFCC ta ayyana tsohon kwamishinan Abia matsayin wanda take nema ruwa a jallo.
Allon da ke gaban hedikwatar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da ke Abuja. Hoto: @officialEFCC
Source: Facebook

EFCC na neman tsohon kwamishinan Abia

Shugaban sashen yada labarai na EFCC, Dele Oyewale ya fitar da sanarwar neman tsohon kwamishinan a shafin hukumar na X a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

DSS ta gurfanar da manyan wadanda ake zargi da hannu a hare-haren jihohi 2 na Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce ana zargin Enweremadu da hannu a cikin badakalar karkatar da kudin jama'a da kuma almundahana.

Dele Oyewale ya bayyana cewa, adireshin Enweremadu na ƙarshe shi ne ma'aikatar kananan hukumomi da masarautu, dake Umuahia, jihar Abia.

Hukumar EFCC ta roki duk wanda ke da masaniya a kan inda Enweremadu yake da ya tuntubi ɗaya daga cikin ofisoshinta na shiyya-shiyya.

Ana zargin tsohon kwamishina da rashawa

Wani bangare na sanarwar ta EFCC, tana cewa:

“Ana sanar da jama’a cewa hukumar da ke yaki da rashawa ta EFCC na neman Christopher Enweremadu, wanda hotonsa ya yake kafe a jikin sanarwar nan, bisa zargin laifin hada baki don karkatar da kudaden jama'a da kuma almundahana.
“Muna fatan duk wanda ke da wani muhimmin bayani kan inda yake, zai tuntuɓi hukumar a ofisoshinta da ke Ibadan, Uyo, Sokoto, Maiduguri, Benin, Makurdi, Kaduna, Ilorin, Enugu, Kano, Lagos, Gombe, Port Harcourt ko Abuja.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun cinnawa gidaje 30 wuta a Filato, mutum 300 sun shiga garari

Jaridar Punch ta rahoto cewa, ko a baya, an gurfanar da tsohon kwamishinan, wanda ya yi aiki a karkashin tsohon gwamnan Abia, Gwamna Okezie Ikpeazu.

Hukumar EFCC ta ce ana zargin tsohon kwamishinan Abia da karkatar da kudin jama'a da kuma almundahana
Jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a bakin aiki. Hoto: @officialEFCC
Source: UGC

An gurfanar da tsohon kwamishina da wasu

A lokacin, an gurfanar da Christopher Enweremadu gaban kotu game da wani bincike kan yadda aka tafiyar da kudaden kananan hukumomin jihar ta Abia.

A Disambar 2024, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin a binciki kudin da aka ware wa kananan hukumomi 17 na Abia tsakanin 2019 zuwa 2023 kuma ta umarci EFCC da ta mika rahoton bincikenta ga kotun.

Har ila yau, Kotun ta ba da umarnin a kwace takardun tafiye-tafiye na kasa da kasa na wasu tsoffin jami'an gwamnati uku, ciki har da tsohon kwamishinan.

Sauran sun hada da wani tsohon hadimin tsohon gwamnan, Erondu Uchenna Erondu, da kuma babbar sakataren ma'aikatar kananan hukumomi da masarautu, Deaconess Joy Nwanju.

EFCC na neman surukin Atiku Abubakar

A wani labarin, mun ruwaito cewa, EFCC ta ayyana Bashir Haske, surukin tsohon Atiku Abubakar, a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.

Kara karanta wannan

Bayan gargadin NEMA, Ambaliya ta afka wa dubban mutane a Adamawa

Hukumar da ke yaki da rashawar, ta bayyana cewa tana neman Haske, ɗan kasuwar da ke da gidaje a Ikoyi da Victoria Island, a jihar Legas.

EFCC ta roƙi al’umma da su ba da duk wani bayani da zai taimaka wajen cafke surukin tsohon mataimakin shugaban kasar, ta hanyar tuntuɓar ofisoshinta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com