Da Dumi-Dumi: Hukumar EFCC Ta Yi Ram da Tsohon Gwamna a Filim Jirgi, Ta Tsare Shi Tare da Dansa
- EFCC ta kama tsohon gwamnan Abia, Theodore Orji, a filin jirgin Nnamdi Azikwe dake Abuja
- Tsohon gwamnan ya jima cikin waɗanda EFCC ke gudanar da bincike a kansu tare da ƴaƴansa
- Hukumar ta na zarginsa da sama da faɗi da wasu kuɗaɗen gwamnati yayin da yake kan mulkin Abia
Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta cafke tsohon gwamnan Abia, Theodore Orji, kamar yadda premium times ta ruwaito.
Tsohon gwamnan, wanda ya jima a jerin sunayen waɗanda EFCC ke bincike a kansu, ya shiga hannu ne a filin jirgin Nnamdi Azikwe, Abuja da misalin karfe 10:00 na safe.
Bayan samun nasarar kama shi ne jami'an EFCC suka yi gaba da shi zuwa hedkwatarsu ta babban birnin tarayya Abuja.
Yanzun haka yana tsare tare da ɗansa, Chinedu, kakakin majalisar dokokin jihar Abia na yanzu, wanda yazo bin ba'asi bayan gano an kame mahaifinsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mista Orji, wanda sanata ne dake kan mulki, da ƴaƴansa biyu, Chinedu da Ogbonna, sun kasance karkashin binciken EFCC na tsawon watanni bisa zargin karkatar da dukiyar al'umma da kuma sama da faɗi da su.
Wane zargi ake wa tsohon gwamnan?
Legit.ng Hausa ta gano cewa ana zargin tsohon gwamnan da karbar miliyan N500 a matsayin kudin tsaro duk wata na tsawon shekara 8 da ya yi akan mulkin jihar Abia 2007-2015.
Sauran zarge-zargen da ake masa sun haɗa da sama da faɗi da biliyan N2bn kuɗin gwamnati da kuma karkatar da kuɗin tsarin Sure-P, kamar yadda punch ta ruwaito.
EFCC ta tabbatar da tsare tsohon gwamnan
Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da tsare tsohon gwamnan da kuma ɗansa kakakin majalisa, amma ya ki bada cikakken bayani.
A watan Fabrairun shekarar 2020, hukumar EFCC ta fara binciken Mista Orji da ɗansa kan zargin yin sama da faɗi da biliyan N521 tsakaninsu.
Binciken ya biyo bayan korafin da kungiyar yakar cin hanci domin ceto Najeriya ta shigar ga EFCC ranar 17 ga watan Maris 2017.
A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Tsohon Sakataren NMA, Sun Nemi a Tattaro Musu Kudin Fansa
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun sace Adedamola Alayaki, a gonar mahaifinsa ranar Laraba.
Hukumar yan sanda reshen jihar Ogun ta tabbatar da faruwar lamarin, tace a halin yanzun jami'anta sun fara bincike.
Asali: Legit.ng