Sabon Tsari: Cikakken Jerin Darussan da Za a Rika Koyarwa a Makarantun Sakandare
- Gwamnatin tarayya ta gabatar da sababbin darussan karatu a makarantun sakandare da za su fara aiki a shekarar karatu ta 2025/2026
- Sabon tsarin karatun da aka kawo ya mayar da hankali ne kan koyar da dalibai fasahar zamani da kasuwanci tun daga matakin JSS
- Darussan da za a rika koyarwa yanzu sun haɗa da Cybersecurity, Python, JavaScript, AI, da kuma koyon yarukan duniya irinsu Sinanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Gwamnatin Tarayya ta fitar da sabon tsarin karatun makarantun sakandare da zai fara aiki a shekarar karatu ta 2025/2026.
Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan kafofin sada zumunta, Dada Olusegun, ya wallafa bayanai game da sauye-sauyen darussan da za aka samu a ranar Laraba.

Source: Getty Images
A shafinsa na X, Olusegun Dada ya wallafa hotuna da ke dauke da cikakken bayani kan darussan da yanzu za a rika koya wa a makarantun sakandare (JSS-SSS).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kawowa sakandare darusan fasahar zamani da kasuwanci
Sabuwar manhajar karatun ta ba da muhimmanci sosai ga ilimin fasahar zamani da dabarun kasuwanci tun daga farkon karatun sakandare.
A matakin JSS, za a koyar da dalibai dabarun ilmin rubuta yaren komfuta kamar Python da Scratch da ake amfani da su wajen kirkirar manhaja da makamantansu.
Hakazalika za a koyawa 'yan kananan sakandare dabarun bincike a intanet da koyon ilimin mutum-mutumi mai sarrafa kanta (robotics).
Haka nan, an saka darussan kasuwanci a cikin Social Studies, da nufin inganta sanin tattalin arziki da kirkire-kirkire a tsakanin matasa.
Rahoton ya kuma bayyana cewa an kawo sababbin shirye-shiryen kwamfuta, fasahar AI da yarukan duniya a matakin babbar sakandare, watau SSS.
Dalibai a matakin SSS za su fuskanci manyan darussa, ciki har da koyon yaren komfuta na Python da JavaScript, da fasahar hankali AI.
Za a rika karantar da ilmin kimiyyar bayanai na Data Science da kuma tsaro a yanar gizo (cybersecurity).
Har ila yau, manhajar ta karfafa koyon yarukan duniya, tare da samar da darussan Faransanci, Larabci, da Sinanci (Sinanci a matsayin zabin da ba dole ba) tare da ci gaban adabi a harshen gida.
Cikakken jerin darussan marakarantun sakadare
A ƙasa akwai cikakken jerin darussan da yanzu za a rika koyar da daliban makarantun sakandare, dafa JSS zuwa SSS:
Karamar Sakandare (JSS1–JSS3)
Mathematics & Measurement (Hisabi da Lissafi)
- Numbers, fractions, decimals, percentages
- Ratios, proportions, rates
- Geometry: angles, area, volume
- Algebra: expressions, equations
- Statistics: mean, median, mode
- Graphs: line, bar, pie
- Measurement: km, m, cm, g, kg, ml, L, °C, time zones
English Language (Ingilishi)
- Essay writing: narrative, descriptive
- Advanced grammar: clauses, idioms
- Comprehension of articles, literature
- Vocabulary: academic & global terms
- Oral: debates, speeches, drama
Integrated Science (Kimiyya)
- Physics: motion, forces, energy
- Chemistry: matter, mixtures, reactions
- Biology: cells, reproduction, ecology
- Earth Science: climate, natural resources
- Technology: electricity, mechanics
- Experiments & lab safety
Digital Literacy & Coding (Ilmin komfuta)
- Word, Excel, PowerPoint
- Internet research & safety
- Coding (Python basics, Scratch advanced)
- Robotics (basic kits)
Social Studies (Ilmin zamantakewa da makamantansu)
- History of Nigeria, Africa
- Geography: maps, lat/long, climate
- Civics: rights, duties, democracy
- Economy: trade, money, entrepreneurship basics
- Global issues: climate change, migration

Kara karanta wannan
Sojojin sama sun yi ruwan bama bamai kan mayakan Boko Haram, an soye 'yan ta'adda
Languages (Harsuna)
- Advanced mother tongue
- Conversational fluency in foreign language (French/Arabic)
Creative Arts (Zane)
- Drawing, painting, crafts
- Drama, theatre, film basics
- Music: reading notes, instruments
Physical & Health Education (Ilmin motsa jiki da kiwon lafiya)
- Advanced sports, fitness training
- Nutrition, reproductive health
- First aid basics
- Drug abuse awareness

Source: Getty Images
Babbar Sakanadare (SS1-SS3)
Mathematics & Advanced Applications (Lissafi)
- Algebra, functions, trigonometry
- Geometry, vectors, bearings
- Calculus: differentiation, integration basics
- Probability, statistics
- Financial mathematics
- Applied mathematics in economics, engineering
English & Communication (Ingilishi da ilmin sadarwa)
Advanced essays, academic writing
Literary analysis, world literature
Critical reading, research skills
Public speaking, presentations
Media, journalism, fact-checking
Sciences (Kimiyya)
- Physics: mechanics, waves, electricity, nuclear physics
- Chemistry: organic, inorganic, industrial, analytical
- Biology: genetics, ecology, biotechnology
- Earth & Environmental Science: sustainability, climate change
Technology & Innovation (Fasaha da kirkira)
- Programming: Python, JavaScript, HTML/CSS
- Data science basics, databases
- AI & robotics intro
- Digital entrepreneurship, freelancing
- Cybersecurity basics
Social Sciences (Ilmin zamantakewa da makamantansu)
- Government & law, constitutions, human rights
- Economics: micro, macro, trade, globalization
- History: Africa, world revolutions, conflicts
- Philosophy & ethics
- Entrepreneurship: business plans, startups
Languages (Harsuna)
- Advanced mother tongue literature
- Fluency in international language (French/Arabic/Chinese optional)
- Creative Arts & Innovation
- Fine art, design
- Music composition, instruments
- Drama & theatre
- Film/media production
Physical & Health Education (Ilmin motsa jiki da kiwon lafiya)
- Professional-level sports training
- Health science, mental health
- Advanced first aid & CPR
- Personal development, leadership
Research & Project Work (Ilmin bincike da nazari)
- Final-year research project
- Hypothesis, data collection, analysis
- Project presentation & defense
Gwamnati ta yi abin a yaba mata - Wakilin dalibai
A zantawar Legit Hausa da Sanusi Ya’u Mani, wakilin daliban Hakimin Mani a jihar Katsina, ya bayyana tasirin sauye-sauyen darussan da gwamnati ta kawo a makarantun sakandare.
Sanusi Ya'u ya ce:
“Wannan sabon sauyi dai abin alfahari ne. Yana nuna cewa gwamnati ta fara kallon makomar yara. A yau ba za ka yi magana ba sai ka ji ana cewa AI ko kuma fasahar zamani, to idan ba mu shirya yara tun daga makaranta ba, yaya za su iya gogayya da takwarorinsu a waje?”
Ya kara da cewa:
“Wannan canji zai taimaka wajen fito da matasa da za su iya dogaro da kansu, ba sai sun tsaya jiran aikin gwamnati ba. Kuma mu a Arewa ya kamata mu fi dagewa saboda mu ne muka fi dogaro da noma da kananan sana’o’i.”
Yanzu da aka samar da wannan sauyi, Wakilin Daliban ya iyaye da cewa:
“Ya kama dai iyaye su dage wajen tura ’ya’yansu makaranta. Domin a gaskiya ilimi shi ne gishirin zaman duniya, shi ne babban jarin da za ka ba ɗanka ya rayu da shi har abada.”
An canja tsarin karatun firamare, sakandare
Tun da fari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Najeriya ta kawo sauye-sauye biyar a kundin tsarin koyarwa na makarantun firamare, sakandare da na fasaha.
Gwamnati ta ce an gabatar da sabon tsarin karatun ne domin rage yawan darussa ga ɗalibai tare da ƙara zurfafa ilimi, don samar da ingantaccen sakamako a gaba.
Karamar ministar ilimi, Farfesa Suwaiba Ahmad, ta ce sauyin ya zama dole, la'akari da cewa dalibai ba sa fahimtar karatu a tsohon tsarin, mai dauke da yawan darussa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



