Manyan Fastoci sun goyi bayan koyon harshen Larabci a Najeriya

Manyan Fastoci sun goyi bayan koyon harshen Larabci a Najeriya

Malaman addinin Kirista a jihar Kaduna sun nuna goyon bayansu ga hukumar koyon larabci da addinin Islama (NBAIS) sannan sun karfafa wa Kiristoci gwiwar koyon harshen Larabci.

Da suke magana a lokacin da suka kai wata ziyarar ban girma zuwa ga hukumar, Shugaban cocin Christ Evangelical Intercessory Fellowship Ministry, Fasto Yohanna Buru, wanda ya jagoranci tawagar ya ce idan Kiristoci suka karanci harshen Larabci, hakan zai karfafa yaduwar zaman lafiya tsakanin Musulmai da Kiristoci.

Buru ya ce: “Harshen Larabci kamar Turanci, Farasanci da sauran yarukan da ake yi a fadin duniya wadanda ake amfani da su wajen sadarwa da tattauna abubuwan da suka shafi kasuwanci ne a fadin nahiyar Afrika."

Malaman addinin na kirista sun bukaci yan Najeriya da su karanci Larabci a matsayin darasi sannan kada su yi ma yaren kallo a matsayin addini cewa, “Kiristoci da yawa da mabiya wasu addinai na yiwa Larabci kallon addini, ba tare da sun san cewa yare bane.”

Ya ce manyan malaman Kiristoci da dama sun koyi yadda ake karatu da rubutun Larabci domin zantawa a Najeriya da sauran yankunan Afrika ta Kudu, sannan ya bukaci sauran jama’a da kada su yi watsi da yaren saboda nasabarsa da addinin Islama.

Da yake martani, Mukaddashin rijistiran hukumar, Farfesa Shafi’u Abdullahi, ya ce da fari hukumar na da makarantu 17 a karkashinta amma a yanzu tana da sama da 1,542 a fadin kasar.

KU KARANTA KUMA: Kai duniya: Yadda dan shekara 15 ya dunga luwadi da yaro dan shekara 6 a Kaduna

Ya kara da cewa wani Kirista ne ya jagoranci kafa sashin koyon Larabci a jami’arr Ahmad Bello cewa, “Muna koyon harshen Laraci a hannun Musulmai da Kiristoci.”

Shafi’u, wanda ya bayyana cewa Najeriya na rasa abubuwa da dama saboda rashin harshen Larabci, ya ce karantar Larabci na da matukar muhimmanci a duniyar yau sannan ya yi kira ga Kiristoci da Musulmai da su koyi yaren domin sadarwa mai karfi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel