An Yi wa Ɗalibar Jami'ar Najeriya Tsirara a gaban Jama'a, Jami'an Tsaro Sun Fara Kame
- ’Yan sandan Bayelsa sun kama wata daliba mai suna Kadi daga Jami’ar Tarayya ta Otuoke, bisa zargin yi wa abokiyar karatunta tsirara
- An ga Kadi tare da wasu ’yan mata a bidiyo suna cin zarafin wata daliba mai suna Nancy, inda suka yi mata duka tare da cire mata kaya
- An ce jami’an tsaro sun yi aiki da umarnin CP Francis Idu tare da taimakon jami’an tsaron jami’ar kafin su kama wadda ake zargi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bayelsa – Rundunar ’yan sanda a Zone 16 ta kama wata daliba daga Jami’ar Tarayya Otuoke (FUO), mai suna Kadi, bisa zargin dukan abokiyar karatunta da yi mata tsirara.
Wannan na zuwa ne bayan wani bidiyo ya yadu a kafafen sada zumunta inda aka nuna yadda Kadi da abokiyarta suka dinga cin zarafi da azabtar da wata daliba mai suna Nancy.

Source: Twitter
An yi wa dalibar jami'a tsirara a bidiyo
Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa an nadi bidiyo kuma aka wallafa shi a Facebook a ranar Lahadi, inda aka ga Kadi da wasu dalibai mata biyu suna lakada wa Nancy duka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan haka, suka cire mata kaya tare da yanke mata gashin kai da wani abu mai kaifi, lamarin da ya tayar da hankula a shafukan sada zumunta.
Ma'abota shafukan sada zumunta sun yi Allah wadai da yadda daliban suka ki duba darajar 'yar uwarsu mace, suka yi mata tsirara gaban jama'a, kuma har aka nadi abun a bidiyo.
Yadda 'yan sanda suka kama Kadi
An rahoto cewa jami’an Zone 16, bisa umarnin kwamishinan ’yan sanda, CP Francis Idu, tare da jami’an tsaron jami’ar FUO, sun kama Kadi.
A cikin wata tattaunawar waya da wani mutum ya nada, kuma ya wallafa a Facebook, Kadi ta tabbatar da cewa jami’an NSCDC ne suka kama ta kuma za a kai ta Zone 16 da ke Yenagoa.

Kara karanta wannan
El Rufai ya nuna yatsa ga Uba Sani bayan 'yan daba sun tarwatsa taron ADC a Kaduna
Da aka tambaye ta ko rikicin na da nasaba da tsohon saurayinta mai suna “Upcoming”, Kadi ta musanta hakan.
Jaridar yanar gizo ta The Network ta rahoto Kadi tana fada wa mutumin cewa:
“Ba shi bane, mun rabu tun wata daya da ya gabata. Abin da ya faru shi ne, wata ce ta zagi kakata, wai tana wari, shi yasa muka yi mata dukan tsiya.”

Source: Original
An yi Allah-wadai da yi wa daliba tsirara
Kungiyar AWAGBV tare da Do Foundation sun bayyana takaici da damuwa kan bidiyon cin zarafin dalibar jami'ar FUO da aka gani a kafafen sada zumunta.
Shugabar AWAGBV, Dr. Dise Harry, ta ce abin kunya ne a ce mata su ne kan gaba wajen nuna irin wannan mummunan hali na tashin hankali.
Ta ce wannan al’amari ya shafi abubuwa masu muhimmanci kamar cin zarafi, raunata jiki, barazana ga rayuwa da kuma dora bidiyon tsiraici na dalibar a intanet.
'Yan sa-kai sun yi wa 'yar NYSC tsirara
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu gungun 'yan sa kai a Anambra, da ake kira da Agunechemba, sun yi wa matashiya mai yi wa kasa hidima tsirara.
A cikin wani bidiyo da ya bazu a intanet, an ga lokacin da 'yan sa kan ke lakada wa 'yar NYSC duka, tare da yaga kayanta har gaba daya tsiraicinta ya fito fili.
Lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a soshiyal midiya, ya sa gwamnatin jihar Anambra ta ba da umarnin cafke jami’an da suka aikata cin zarafin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

