Bidiyon soja yana dukan budurwa tare da yi mata tsirara a titi kan shigar banza

Bidiyon soja yana dukan budurwa tare da yi mata tsirara a titi kan shigar banza

- Wani soja ya jibgi wata budurwa, a kan ta yi mummunar shiga

- Ya finciki gashinta kuma ya yi kokarin tube mata rigar nono

- Allah ne ya taimaketa da masu wucewa suka dakatar da shi

Wani soja wanda ba a gano sunansa ba, ya cutar da wata mata a ranar Asabar, inda yace ta yi shigar banza.

Al'amarin ya faru da misalin 9:47am a Oju-Ore a wuraren Ota da ke jihar Ogun.

Budurwar ta sanya wata riga gajera da kuma wata rigar saka a samanta, inda ta fuskanci cutarwar tana cikin tafiya.

Bidiyon soja yana dukan budurwa tare da yi mata tsirara a titi kan shigar banza
Bidiyon soja yana dukan budurwa tare da yi mata tsirara a titi kan shigar banza. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

Wani ganau ya tabbatar wa da The Punch cewa sojan yana cikin tuka wata babbar mota ya fito daga motar ya hau dukanta.

KU KARANTA: Hotunan ranar daurin auren jarumi Nuhu Abdullahi da zukekiyar amaryarsa

Ya bayyana yadda sojan ya dauke budurwar da mari, bayan ta yi kokarin tserewa ya janyota tare da fizgar gashinta.

A wani bidiyo, an ga inda sojan yayi yunkurin tube wa budurwar rigarta tare da fizgar rigar nononta, tukunna masu wucewa suka kwace ta. Sun yi ta rokonsa, da kyar ya kyaleta.

KU KARANTA: Gagarumin rikici ya barke bayan 'yan daba sun fada kotu tare da fatattakar alkali da lauyoyi

Daga baya ya koma cikin motar hayar wacce yake tukawa ya wuce.

An yi kokarin tattaunawa da kakakin 81 Division na sojin Najeriya, Olaniyi Osoba, don a ji ta bakinsa a ranar Asabar, amma wayarsa a kashe.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta zargi sojojin Najeriya da cin zarafin jama'a, kisa ba tare da kotu ta bayar da umarni ba, aski ba bisa ka'ida ba, da sauran laifuka.

A wani labari na daban, wasu mutane dauke da makamai da ake zargin 'yan bindiga ne sun tarwatsa masu kada kuri'a a kauyen Oroji da ke gundumar Rini ta karamar hukumar Bakura da ke jihar Zamfara a ranar Asabar.

Lamarin ya faru a ranar Asabar yayin da ake zaben maye gurbi na majalisar dattawa, kamar yadda rahoto daga HumAngle ya bayyana.

Jaridar Daily Trust ta bayyana yadda wani mai kada kuri'a mai suna Sulaiman Muhammad, yake sanar da cewa lamarin ya faru wurin karfe 8:30 na safe yayin da ake dab da fara saka kuri'u.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel