'Kalamanka na da Haɗari,' CAN Ta Taso El Rufai a gaba kan Yawan Kiristocin Kaduna
- Shugaban CAN na jihohin Arewa da Abuja, Rev. John Hayab, ya soki furucin Nasir El-Rufai kan adadin Kiristoci da ke Kaduna
- Tsohon gwamna, Nasir El-Rufai ya yi ikirarin cewa gaba daya mutanen Kudancin Kaduna ba su kai 25% na yawan jama’ar jihar ba
- Rev. Hayab ya ce kalaman 'dan siyasa barazana ce ga hadin kan Kaduna, kuma suna da hadari musamman ganin cewa ya saba lamba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) a jihohin Arewa 19 da Abuja, Fasto John Joseph Hayab, ya soki tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, kan kalamansa game da yawan jama’ar Kudancin Kaduna.
Hayab ya bayyana cewa furucin tsohon gwamnan abin takaici ne, mai cike da rarrabuwar kai, kuma ba zai taimaka wajen kawo zaman lafiya da haɗin kai ba.

Source: Twitter
Kalaman El-Rufai sun tayar da ce-ce-ku-ce
A wata hira da aka yi da shi a tashar Channels TV, El-Rufai ya ce al’ummar Kudancin Kaduna ba su kai 25% na yawan jama’ar jihar ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma ce bai yi nadama ba game da manufofi da matakan da ya ɗauka a lokacin mulkinsa wanda suka shafi al’ummar yankin, kamar yadda muka ruwaito.
Sai dai, shugaban CAN, Rev. Hayab ya ce kididdigar da aka taba yi a baya ta nuna cewa Kudancin Kaduna na da adadi mai yawa na jama’a.
Ya yi nuni da yadda iyalai a yankin ke da yara da yawa, har ana samu mutane 15 zuwa 23 a gida ɗaya, wanda ke nuna karfin jama’ar yankin.
Zargin sauya alkaluma a wasu yankuna
Shugaban al'ummar Kiristocin ya yi zargin cewa matsalar ba ta ƙarancin jama’a ba ce a Kudancin Kaduna, illa dai akwai matsalar alkaluman kididdigar da ba a sabunta ba.

Kara karanta wannan
El Rufai ya tsokano Ministan Abuja bayan ya yi hasashen makomar Tinubu a zaben 2027
Ya ce irin wannan matsalar ce ta janyo rashin adalci ga yankin, musamman ma a wajen rabon albarkatun jiha.
Jaridar Vanguard ta rahoto Rev. Hayab ya nuna takaici kan yadda El-Rufai ya ce bai yi nadama ba kan manufofin da suka jefa Kudancin Kaduna a mawuyacin hali
Ya ce kalaman tsohon gwamnan hadari ne ga hadin kan jama'a, musamman ganin yadda jihar ke samun natsuwa a yanzu fiye da lokacin mulkinsa.

Source: Twitter
Kira ga adalci da gaskiya nan gaba
Hayab ya bukaci gwamnatin tarayya da idan ta tashin yin kidaya a nan gaba, ta sanya addini da kabila domin guje wa rudani game da alkaluman kididdigar.
Ya kuma roki ’yan Najeriya da su guji biye wa maganganu da labaran da ke jawo rarrabuwar kawuna, su rungumi adalci, gaskiya da hadin kai domin dorewar zaman lafiya.
Za a kafa jami'a a Kudancin Kaduna
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Bola Tinubu ta amince a kafa jami'ar tarayya a Kudancin Kaduna domin magance bukatun ilimi da ci gaban yankin.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana haka tare da cewa gwamnati na kuma duba yiwuwar kafa cibiyar lafiya a Kafanchan, da ke jihar.
Kashim Shettima ya jaddada goyon bayan shugaban kasa Bola Tinubu ga ci gaban Kudancin Kaduna, yana kuma yabawa gwamnatin jihar karkashin Uba Sani.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

