An Kwashi Gawar 'Yan Bindiga a Buhu bayan Sojoji Sun Kashe 'Yan Ta'adda 50
- Jami’an tsaro sun yi nasarar kashe akalla ‘yan bindiga 50 a kauyen Kumbashi na karamar hukumar Mariga
- ‘Yan bindiga kimanin 300 dauke da makamai suka yi yunkurin kai hari amma jami’an tsaro suka fatattake su
- Kakakin majalisar dokokin jihar ya jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin al’umma da jami’an tsaro
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A kalla ‘yan bindiga 50 ne suka rasa rayukansu a wani artabu da jami’an tsaro suka yi da su a kauyen Kumbashi da ke karamar hukumar Mariga a Jihar Neja.
Rahoto ya nuna cewa hadin gwiwar sojojin Najeriya da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ne ya kai ga nasarar fatattakar mayakan da suka zo dauke da mugayen makamai domin kai hari.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa shugaban majalisar dokokin jihar, Abdulmalik Mohammed Sarkin-Daji, wanda ke wakiltar mazabar Mashegu, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kashe 'yan ta'adda 50 a Neja
Shaidun gani da ido a Kumbashi sun bayyana cewa kimanin ‘yan bindiga 300 dauke da makamai masu sarrafa kansu suka dira kauyen da misalin karfe 3:00 na rana a ranar Talata.
An ce manufar harin ita ce kai farmaki kan sansanin jami’an DSS da ke yankin, sai dai jami’an tsaro sun yi gaggawar maida martani da kyau.
Artabun ya dauki tsawon lokaci, amma kwarewar jami’an tsaro ta bai wa rundunar damar kashe akalla ‘yan bindiga 50, yayin da da dama suka tsere dauke da raunukan harbin bindiga.
An saka gawar 'yan bindiga a buhu
Rahotanni sun ce bayan artabun, an ga ‘yan bindiga suna daukar gawarwakin abokan nasu da suka mutu sannan suka lullube su cikin buhuna.
Daily Post ta wallafa cewa daga nan sai suka dauke gawarwakin a kan babura suka fice daga yankin domin gujewa barin su a wurin.
Martanin shugaban majalisar Neja
Abdulmalik Sarkin-Daji ya bayyana cewa nasarar da aka samu a Kumbashi ta nuna karfin dabaru da makaman jami’an tsaro da suka fi na ‘yan ta’adda.
Ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar samar da sahihan bayanai cikin gaggawa domin ci gaba da samun nasara a yakin da ake yi da miyagu.
Hakazalika, ya tabbatar da cewa majalisar dokokin jihar za ta ci gaba da goyon bayan duk abin da zai inganta ayyukan tsaro a fadin Jihar Neja.

Source: Facebook
Shugaban majalisar ya ce gwamnatin jihar da ‘yan majalisar suna tare da jami’an tsaro wajen yaki da ‘yan bindiga, don haka al’umma su rungumi tsarin bayar da bayanai.
An sace mutum 100 a jihar Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa an kai wasu munanan hare hare a kauyukan jihar Zamfara da suka jawo asarar rayuka.
Wani rahoto na musamman ya nuna cewa maharan sun sace mutane akalla 100, ciki har da mata da yara kanana.
Wasu mazauna yankunan da aka kai harin sun tabbatar da cewa maharan sun musu barna sosai tare da kira ga gwamnat ta dauki mataki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


