Ana Hallaka Jama'ansa, Gwamna Radda Zai Kashe Naira Miliyan 680 a Gyaran Maƙabartu
- Za a kashe kimanin Naira miliyan 680 a gyaran makabartu a kananan hukumomi 34 na Katsina, jihar da musulunci ke da tarihi
- Gwamna Dikko Radda ya ce za a hannanta wa kowanne ciyaman Naira miliyan 20 don ya je ya gyara makabartun da suka lalace
- Wannan na zuwa ne 'yan kwanaki kadan, bayan da wasu 'yan bindiga suka kashe sama da mutane 30 a masallacin Garin Mantau
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta amince da ware Naira miliyan 20 ga kowace karamar hukuma domin gyara makabartu a yankunanta.
Gwamna Dikko Umaru Radda ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis lokacin da ya gana da sarakunan gargajiya daga masarautun Katsina da Daura a fadar gwamnati.

Source: Twitter
Gyaran makabartu da fara biyan alawus
Ya ce wannan mataki ba wai kawai hidima ce ga al’umma ba, har ma wata hanya ce ta neman albarkar Allah ga jihar Katsina, a cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baya ga ba da kudin gyaran makabartu, Gwamna Dikko Radda ya sanar da shirin fara biyan sabon tsarin alawus da ya ce zai ƙarfafa sarakunan gargajiya da malamai a fadin jihar
A cewarsa, dokar da majalisar dokoki ta jihar ta amince da ita ta tanadi cewa, dukkan Hakimai za su riƙa karɓar albashin da bai gaza da matakin aiki na 'Grade Level 16' ba.
Haka kuma, za a rika ba dagattai, ko masu unguwanni alawus, yayin da su ma limamai sama da masallatai 3,000 da mataimakansu za su rika samun nasu kudin.
Baya ga haka, masu share masallatan Izala da Darika a kowace karamar hukuma 34 suma za su amfana daga wannan tallafi.
Kokarin Gwamna Radda kan tsaro
Gwamnan jihar Katsina ya sake nanata cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko wajen yaki da rashin tsaro da ke addabar jihar.
Ya bayyana cewa, an riga an horar da matasa sama da 1,500, tare da basu kayan aiki don su tallafa wa hukumomin tsaro.
Premium Times ta rahoto gwamnan yana cewa, dole ne al’umma ta fara taimaka wa kanta kafin a iya ganin kokarin da gwamnati take na dogon lokaci.
“Tsaro alhakin kowa ne, dole mu haɗa kai wajen kare jama’armu,” inji Dikko Radda.
Sarakuna suna goyon bayan Gwamna Radda
Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq-Umar, wanda Hakimin Baure, Alhaji Daha Umar-Farouq ya wakilta, ya tabbatar da goyon bayansu ga gwamnan.
Haka kuma, Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Ida, wanda ya wakilci Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir-Usman, ya yaba wa gwamnan bisa irin gyare-gyaren da ya kawo wanda suka dawo da martabar masarautu.
Ya ce gyare-gyaren sun ƙara karfafa matsayin sarakunan gargajiya a sha’anin mulki da ci gaban al’umma.
Majalisun masarautu sun yi alkawarin ci gaba da ba da goyon baya da addu’o’i domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a fadin jihar Katsina.

Source: Twitter
'Yan bindiga sun kashe masallata a Katsina
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun hallaka fiye da mutane 30 a harin da suka kai kan mutane da ke yin Sallah a cikin wani masallaci a Garin Mantau, jihar Katsina.
Mutanen da suka tsira daga harin da 'yan bindigar suka kai, sun ce miyagun sun farmake su ne a daidai lokacin da suke yin Sallar Asuba.
Majiyoyi sun nuna cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu a wannan harin ya zarce mutum 30, sabanin mutane 13 da gwamnati ta ce sun rasu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


