'Shi ne Zaɓin Jama'a,' Gwamna Ya Naɗa Sabon Sarkin Zuru bayan Mutuwar Mai Martaba

'Shi ne Zaɓin Jama'a,' Gwamna Ya Naɗa Sabon Sarkin Zuru bayan Mutuwar Mai Martaba

  • Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris ya amince da Sanusi Mikailu a matsayin sabon sarkin Zuru, bayan tantancewar masu naɗin sarki
  • Gwamnati ta bayyana cewa mutane uku ne suka tsaya takarar kujerar sarkin, kuma Sanusi ya samu mafi rinjayen kuri, da ya ba shi nasara
  • Yanzu za a riƙa kiran sabon sarkin da Sanusi Mikailu Sami Gomo III, bayan ya gaji sarautar daga Muhammadu Sani Sami da ya rasu a London

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kebbi - Masarautar Zuru ta yi sabon sarki, ƴan kwanaki bayan rasuwar mai martaba Sarki Muhammadu Sani Sami Gomo II.

Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris ya amince da da naɗin Sanusi Mikailu a matsayin sabon sarkin Zuru, don ya gaji marigayi Muhammadu Sani.

Gwamna Nasir Idris ya amince da naɗin Sanusi Mikailu a matsayin sabon sarkin Zuru.
Sanusi Mikailu, sabon sarkin Zuru zaune a cikin wani gida. Hoto: Kakakin Cikin Gida
Source: Facebook

Gwamna ya nada sabon Sarkin Zuru

Kara karanta wannan

Ko sun yi ritaya, Tinubu ya amince a cigaba da biyan wasu manyan jami'ai albashi

Babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan, Ahmed Idris, ya sanar da da wannan naɗi a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 28 ga watan Agusta, 2025, inji rahoton Punch.

Sanarwar ta rahoto cewa majalisar masu zaɓen sarki ce ta gabatar da sunan Sanusi Mikailu, bayan tantance waɗanda suka nemi zama sarkin Zuru.

"Naɗin ya biyo bayan matakan sarauta da aka bi na zaben sarki, inda Sanusi Mikailu ya samu kuri'u bakwai cikin tara na masu zaben sarki a masarautar Zuru," a cewar sanarwar.

An mika takardar nadi ga sabon sarkin Zuru

An rahoto cewa, kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu na jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Dutsin Mari ne ya mika wa Sanusi Mikailu takardar naɗin a garin Zuru.

Da ya ke mika takardar naɗin, Alhaji Abubakar Dutsin Mari ya fayyace cewa, Sanusi Mikailu ya zama sabon sarkin Zuru ne ta hanyar sahihin zabe, kuma bisa cancanta.

Kwamishinan ya ce:

"Ƴan takara uku ne suka nemi kujerar sarki, amma shi (Sanusi Mikailu) ya samu nasara bayan samun mafi yawan kuri'u. Duk abin da mutanenmu suke so ne muka yi kokarin yi."

Kara karanta wannan

Duniya labari: Tsohon shugaban hukumar Kwastam kuma Sardaunan Adamawa ya rasu

Gwamnatin Kebbi ta ce ta amince da nadin Sanusi Mikailu saboda shi ne zabin da jama'a suke so
Gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idris yana jawabi a wani taro da aka yi a Birnin Kebbi. Hoto: @KBStGovt
Source: Facebook

Sabon Sarkin Zuru mai kaunar jama'a

Sanarwar da aka wallafa a shafin gwamnatin Kebbi na X, ta rahoto Alhaji Abubakar Dutsin Mari ya yi magana game da zabin al'umma, yana mai cewa:

"Nasararsa ta nuna ƙaunarsa ga jama'arsa, kuma jama'arsa suna ƙaunarsa, mu kuma za mu ƙaunaci wanda al'umma suka zaba."

Kwamishinan ya gode wa Gwamna Nasir Idris bisa amincewa da naɗin, kuma ya buƙaci sabon sarkin ya ba marar ɗa kunya a wannan sabon muƙami da ya samu.

Rahoto ya bayyana cewa, daga yanzu za a rika kiran Sanusi Mikailu, da sunan Sarki Sanusi Mikailu Sami Gomo III.

Sarkin Zuru, Muhammadu Sani Sami ya rasu

Tun da fari, mun ruwaito cewa, jihar Kebbi ta yi babban rashi bayan sanar da rasuwar Mai Martaba Sarkin Zuru, Muhammadu Sani Sami Gomo II.

Sarkin Zuru, Janar Muhammad Sani, tsohon gwamnan soja na Bauchi, ya riga mu gidan gaskiya a ranar Asabar, 16 ga Agusta, a wani asibitin London.

Marigayin ya shiga aikin soja a 1962, ya yi horo a Najeriya da kasashen waje, kafin a nada shi gwamnan Bauchi bayan juyin mulki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com