Shugaba Buhari ya jinjinawa Sarkin Zuru yayin cikarsa shekaru 75 a Duniya

Shugaba Buhari ya jinjinawa Sarkin Zuru yayin cikarsa shekaru 75 a Duniya

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito mun samu rahoton cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika da sakonninsa na taya murna gami da jinjina ga Sarkin Zuru, Alhaji Muhammadu Sani Sami yayin cikarsa shekaru 75 a duniya.

Cikin wata sanarwa ta kakakin shugaban kasar, Femi Adesina ya bayyana cewa, shugaba Buhari yana taya murna gami da jinjina ta ban girma dangane da wannan munzali na rayuwa da Sarkin Zuru ya taka a bisa yiwa al'umma hidima.

Shugaba Buhari ya yi tarayya da masarautar Zuru, gwamnati da kuma Al'ummar jihar Kebbi, 'yan uwa da abokan arziki wajen taya murna ga Uban kasar da ya shafe tsawon rayuwarsa wajen jagoranci da yiwa al'ummar sa hidima maras yankewa.

Shugaba Buhari ya jinjinawa Sarkin Zuru yayin cikarsa shekaru 75 a Duniya
Shugaba Buhari ya jinjinawa Sarkin Zuru yayin cikarsa shekaru 75 a Duniya
Asali: Depositphotos

Shugaban kasar ya hikaito yadda Alhaji Sami ya kafa wasu muhimman ayyuka na noma domin habaka tattalin arziki da kuma inganta harkokin ilimi musamman wajen kara karfin gwiwa ga Matasa akan neman ilimi da neman na kansu.

KARANTA KUMA: Wani Mummunan Hatsari ya salwantar da rayuwar wata Mahaifiya da Jariran ta 2 a jihar Akwa Ibom

Shugaba Buhari ya kuma roki mai duka akan ya ja zamanin Alhaji Sami cikin koshin lafiya domin ci gaba da hidima ga al'ummar sa.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, an cafke wani Mai gadin Coci dauke da kayan Sojoji 6 a jihar Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel