Ko Sun Yi Ritaya, Tinubu Ya Amince a Cigaba da Biyan Wasu Manyan Jami'ai Albashi

Ko Sun Yi Ritaya, Tinubu Ya Amince a Cigaba da Biyan Wasu Manyan Jami'ai Albashi

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da wata sabuwar doka, wacce za ta ba manyan jami'ai damar ci gaba da karbar albashi bayan ritaya
  • Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo ya sanar da hakan a taron baje kolin nasarorin da ma'aikatar ta samu a Abuja
  • Dr. Tunji-Ojo ya ce Tinubu ya yarda a ci gaba da biyan mataimakan kwanturola, kwanturola da wasu jami'ai albashi har zuwa mutuwarsu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya amince a ci gaba da biyan wasu manyan jami’an tsaro albashi har zuwa tsawon rayuwarsu.

Jami'an da za su samu wannan tagomashi sun shafi masu mukamin mataimakin kwanturola, kwanturola, babban kwamanda zuwa sama.

Shugaba Bola Tinubu ya amince a cigaba da biyan manyan jami'ai albashi ko da sun yi ritaya
Shugaba Bola Tinubu na rattaba hannu kan wata takarda a filin wasa na kasa da ke Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Bola Tinubu ya amince da sabuwar doka

Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ya sanar da hakan a Abuja, yayin taron tattaunawa da ministoci, a cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

"Ba zai yiwu ba": Minista ya fadi kuskuren da Tinubu zai yi da bai cire tallafin fetur ba

Dr. Tunji-Ojo ya ce shugaban kasar ya amince da sabuwar doka, wacce ta ba manyan jami'an tsaron damar ci gaba da karɓar albashi bayan sun yi ritaya.

Ministan ya ce manufar wannan sabuwar doka ita ce inganta walwalar jami’an tsaro, kuma ta yi dai dai da burin Shugaba Tinubu na daga darajar aikin damara.

Ya kuma jaddada kudirin gwamnatin Tinubu na ƙarfafa ayyuka da inganta cibiyoyin gwamnati da ke a ƙarƙashin ma’aikatar harkokin cikin gida.

Goyon bayan Tinubu ga ma'aikatar cikin gida

Wannan bayani ya fito ne cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama'a na hukumar FFS, DCF PO Abraham, ya fitar a ranar Alhamis bayan kammala taron.

A cikin sanarwar, ministan ya bayyana godiya ta musamman ga Shugaba Tinubu bisa goyon bayansa mara yankewa ga ma'aikatar.

Sanarwar ta ce:

“Ministan ya nuna matuƙar godiya ga Shugaba Tinubu saboda goyon bayansa da ba ya yankewa, yana mai tabbatar da cewa dukkanin hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar harkokin cikin gida suna cin gajiyar shirin Renewed Hope.”

Kara karanta wannan

'Abin da ba ku sani ba': Tinubu ya fadi babban abin da ya cimma bayan hawa mulki

Tunji-Ojo ya ce an riga an shafe dogon tarihin jinkirin kara wa jami’ai matsayi, inda ya bayyana cewa jami’ai fiye da 50,000 aka ɗaukaka matsayinsu cikin shekaru biyu kacal.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya ce Tinubu na ba ma'aikatar goyon baya yadda ya kamata.
Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo yana jawabi a wani taron jami'an ma'aikatar a Abuja. Hoto: @MinOfInteriorNG
Source: Facebook

Za a inganta ayyukan hukumar kashe gobara

Ya kuma jaddada cewa a nan gaba, za a dawo amfani da sabon tsari, inda jami'ai za su samu karin matsayi ne kawai bisa ingancin aiki da ƙwarewar da suka nuna.

Ministan ya kuma ce an ƙirƙiri sababbin takardun koyarwa, kuma ana kan gina sabuwar makarantar horar da ma’aikata mai suna Fire Academy, wacce za ta yi gogayya da manyan makarantun duniya, musamman kwalejin kashe gobara ta Arizona da ke Amurka.

Haka kuma, ya umarci hukumar kashe gobara ta tarayya da ta ƙara shiga haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu domin ƙara inganta ayyuka, gina sababbin gine-gine, da kuma zamanantar da harkokin kashe gobara a Najeriya.

Gwamnati tarayya ta kori wasu ma'aikata

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnati ta sallami jami'ai 15 na hukumar gidajen gyaran hali ta ƙasa (NCoS) tare da ragewa wasu ma'aikata 59 girma.

Kara karanta wannan

'An bar Arewa a baya,' Remi Tinubu za ta bude kamfani a Legas, an fara korafi

A wata sanarwa da kakakin hukumar, Umar Abubakar ya fitar, ya ce an ɗauki wannan matakin saboda jami'an sun aikata laifuffuka da rashin ɗa'a.

Umar Abubakar, ya ce ƙarƙashin jagorancin ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, hukumar za ta tabbatar da cewa jami'anta na bin ƙa'idoji.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com