Gwamnatin Tinubu Ta Faɗi Ranar da Za a Kammala Ɗaukar Sababbin Ma'aikata a Hukumar FFS

Gwamnatin Tinubu Ta Faɗi Ranar da Za a Kammala Ɗaukar Sababbin Ma'aikata a Hukumar FFS

  • Za a kammala aikin ɗaukar sababbin ma'aikatan da ake yi yanzu haka a hukumar kashe gobara ta tarayya (FFS) ranar 15 ga watan Afrilu
  • Ministan harkokin cikin gida kuma shugaban majalisar gudanarwa, Olubumi Tunji-Ojo ne ya faɗi haka a wurin ganawa da shugabannin hukumomi 4
  • Tunji-Ojo ya ce waɗanda suka tsallake kuma sunayensu suka fita za a tura masu sako a Email ko kuma ta wayar salula

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Ministan harkokin cikin gida kuma shugaban majalisar gudanarwa, Olubumi Tunji-Ojo, ya yi ƙarin bayani kan ɗaukar ma'aikata a hukumar kashe gobara (FFS)

Ya ce aikin ɗaukar sababbin ma'aikata da ake ci gaba da yi yanzu haka a hukumar kwana-kwana za a karkare shi a ranar 15 ga watan Afrilu, 2024.

Kara karanta wannan

DHQ: Sojoji sun kashe wasu daga cikin ƴan bindigar da suka sace ɗaliban Kuriga

Motocin hukumar kashe gobara FFS.
Za a gama ɗaukar ma'aikata a FFS a watan Afrilu Hoto: Fedfireng
Asali: Facebook

Tunji-Ojo ya ce sabuwar ranar ta yi daidai da wa’adin da majalisar ta tsara gudanar da ayyukan ɗaukar sababbin ma’aikata da ke karkashinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda za a tuntubi wadanda sunayensu suka fita

Ministan ya ƙara da cewa za a bukaci wadanda aka zaba su ziyarci shafin yanzar gizo na hukumar ta sakonnin imel da lambobin wayarsu, inji rahoton Daily Trust.

Sakataren hukumar kula da hukumomin sibil difens, gidan yari, kwana-kwana da shige da fice (CDCFIB), Ja'afaru Ahmad ne ya wakilci ministan a wurin taro da shugabannin hukumomin 4.

Kamar yadda Leadership ta ruwaito, ya yi bayanin cewa waɗandada aka zaba za su zauna jarabawar kwamfuta (CBT) da tantancewar jiki/takaddun shaida da halitta.

Ya kuma yi kira ga ɗaukacin ƴan Najeriya cewa su yi fatali da saƙonnin da ke yawo a soshiyal midiya wanda aka nemi su biya wasu kuɗi domin a ɗaukensu aikin.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito, Shugaba Tinubu ya ba da tallafin makudan kuɗi domin rage kuɗin Hajji 2024

Tunji-Ojo ya kara da cewa irin wadannan sakonnin daga masu damfara ya fito amma ba daga hukumar ba.

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Tinubu

A wani rahoton kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu , GCFR, shugaban Najeriya na yanzu, ya yi bikin cika shekaru 72 da haihuwa a ranar Jumu'a, 29 ga Maris, 2024.

A wannan lokaci na bikin cikarsa shekaru 72 a duniya, Legit Hausa ta tattaro muku abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Shugaba Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel