"Ana Barazana ga Rayuwata," Shugaban NNPCL Ya Tona Masu Son Raba Shi da Mukaminsa

"Ana Barazana ga Rayuwata," Shugaban NNPCL Ya Tona Masu Son Raba Shi da Mukaminsa

  • Shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Bayo Ojulari, na fuskantar bazarana daga wasu masu karfi a masana'antar mai
  • Bayo Ojulari ya ce yanzu haka ana farautar rayuwarsa da ta wasu manyan jami'an NNPCL saboda cika umarnin Shugaba Bola Tinubu
  • Yayin da ya gana da 'yan kungiyar PENGASSAN a ofishinsa a Abuja, Ojulari ya fadi yadda ake kokarin tsige shi daga mukaminsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wasu da ba a san ko su waye ba suna harin rayuwar shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Bayo Ojulari, da na sauran manyan jami’an kamfanin.

Bayo Ojulari ne da kansa ya bayyana hakan a lokacin da ya karɓi tawagar kungiyar ma'aikatan fetur da gas ta Najeriya (PENGASSAN) a ofishinsa a Abuja.

Shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari ya ce ana farautar rayuwarsa da ta manyan jami'an kamfanin
Shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari yana jawabi a taron shugabannin tsaro na kasashen Afrika a Abuja. Hoto: @nnpclimited
Source: Twitter

Ana barazana ga rayuwar shugaban NNPCL

Kara karanta wannan

Ina makomar Tinubu?: APC ta ce za ta ba kowa dama ya tsaya takarar shugaban ƙasa

Jaridar Vanguard ta rahoto manyan ma'aikatan sun ziyarci hedikwatar NNPCL ne bisa jagorancin shugaban kungiyarsu, Kwamared Festus Osifo.

An ji shugaban kamfanin na NNPCL yana cewa ana farautar rayuwarsa saboda ya fara aiwatar da wasu sauye-sauye a harkar man fetur da iskar gas.

Ya ce kuma ya fara aiwatar da sauye-sauyen ne bisa umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya ba shi na farfaɗo da matatun mai da suka durƙushe.

Bayo Ojulari ya yi zargin cewa wasu manya da ke da karfi a masana’antar mai na ƙoƙarin ganin an tumɓuke shi daga kan kujerar shugabancin NNPCL saboda waɗannan sauye-sauye.

NNPCL za ta farfado da matatun gwamnati

Shugaban NNPCL din ya ce tuni aka fara ƙoƙarin farfaɗo da tsofaffin matatun mai da suka jima a rufe domin su dawo suna aiki da cikakken ƙarfinsu.

Ya kara da cewa NNPCL yana nazarin tsarin da NLNG ke amfani da shi wajen gudanar da ayyukansa, domin ganin an yi amfani da irin wannan salo wajen sabunta matatun mai.

Kara karanta wannan

Kudin fansa: 'Yan bindiga sun dauke mutum 4700, an ji biliyoyin da aka rasa a shekara 1

Bayo Ojulari ya kuma yi martani ga kalaman shugaban kungiyar PENGASSAN kan bukatar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin NNPCL da masana’antar man fetur baki ɗaya.

Ya jaddada cewa duk da barazanar da ke kan rayuwarsa da ta manyan jami’an kamfanin, ya ɗauki alhakin tabbatar da cewa matatun mai sun dawo aiki a kasar.

Shugaban kamfanin NNPCL ya bayyana kokarin da ake yi na farfado da matatun man Najeriya
Shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari yana jawabi a taron baje kolin nasarorin NNPCL a fannin makamashi a Abuja. Hoto: @nnpclimited
Source: Twitter

Shugaban kamfanin NNPCL ya aika sako

Jaridar Daily Post ta rahoto Ojulari yana cewa:

“Ni ba na ɓoye wa kowa komai. Ni ba dan siyasa ba ne, amma na fahimci akwai bukatar in ƙara koyon wasu dabaru na siyasa.
"To sai dai, sha'ani na gyaran matatun mai wani shiri ne na ci gaban ƙasa, a kan wannan, na shirya yin tukuru domin ganin an cimma nasarar farfado da su.”

Ojulari ya yi kira ga ’yan ƙasa da ma’aikatan kamfanin da su ci gaba da goyon bayan gyare-gyaren da NNPCL ke yi.

Ya bayyana cewa nasarar farfaɗo da matatun mai zai rage dogaro da shigo da mai daga waje, tare da sauƙaƙa wa talakawa a harkar sufuri da wutar lantarki.

Kara karanta wannan

'APC da PDP sun tafka kuskure, da yiwuwar su sha kaye a zaben shugaban kasa na 2027'

'Da hannun kungiyoyin waje a satar mai'

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban NNPCL, Bayo Ojulari ya ce akwai hannun kungiyoyin kasashen waje a satar man da ake yi Najeriya.

Bashir Bayo Ojulari ya ce a baya kudin shigar man Najeriya ya ragu saboda satar mai, fasa bututu da gina haramtattun matatu a kasar.

Amma shugaban NNPCL din ya ce Najeriya ta kusa cimma 100% na samar da danyen mai sakamakon haɗin kai da hukumomin tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com