Majalisar dattijai ta bankado batan N1.05bn daga asusun hukumar NLNG

Majalisar dattijai ta bankado batan N1.05bn daga asusun hukumar NLNG

A yau, Alhamis, ne kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin kamfanin dillancin man fetur na kasa (NNPC) ya ce babu N1.05bn a asusun adana ribar da hukumar makamashin gas ta kasa (NLNG).

Sanata Bassey Akpan, shugaban kwamitin kula da NNPC a majalisar dattijai, tare da Mista Isiaka Abdulrazaq, jami'in adana kudaden hukumar NNPC ne suka bayyana hakan yayin wata ganawar su a Abuja.

Sai dai Akpan da Abdulrazaq sun bayyana cewar sabanin rahotannin kafafen yada labarai dake nuna cewar kudin sun yi batan dabo ne, hukumar NNPC tayi amfani da kudaden ne wajen sayo tataccen man fetur daga kasashen ketare.

An gudanar da ganawa tsakanin kwamitin majalisar dattijai da jami'an NNPC ne domin cigaba da bincike a kan kudaden hukumar NLNG da Sanatocin ke yi.

Majalisar dattijai ta bankado batan N1.05bn daga asusun hukumar NLNG
Maikanti Baru
Asali: UGC

Legit.ng ta fahimci cewar yanzu maganar binciken ta koma matakin kokarin gano ko kamfanin NNPC na da hurumin yin amfani da kudaden domin sayen tataccen man fetur.

Shugaban NNPC, Maikanti Baru, da kansa ya tabbatar da amfani da kudaden ga majalisar ta dattijai, yana mai bayyana cewar NNPC ta dauki wannan mataki ne bayan cire bayar da tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi a shekarar 2016.

DUBA WANNAN: Harin Boko Haram: An tabbatar da mutuwar Kaftin Kabiru Hamza

Ya ce sun yi hakan ne bisa dogaro da dokar kamfanin NNPC da ta bata damar yin amfani da kudadenta domin gudanar da aiyukan kamfanin.

Sai dai majalisar dattijai ta nuna shakku a kan hakan tare da bayyana cewar kudaden mallakar gwamnatoci ne a mataki daban-daban, a saboda haka NNPC bata da ikon yin gaban kanta wajen yin amfani da kudaden.

A karshen ganawar tasu, Sanata Akpan ya bukaci manema labarai dake wurin taron da su wallafa rahoton gaskiya a kan batun, ba tare da tauye wasu ba

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel