'Yar Najeriya, Hajara Yakubu Ta Doke Yan Kasashe da Dama, Ta Samu Kyaututtuka a India
- Matashiya daga jihar Neja ta sa Najeriya alfahari yayin da ta kammala karatun digiri na farko a jami'ar kasar Indiya
- Dalibar mai suna Hajara Yakubu Jibri' ta samu kyaututtuka da dama saboda bajintar da ta yi a fannin ilimin magunguna
- Hajara ta samu lambar yabon daliba mafi hazaka daga Afirka da wasu kyaututtuka da suka shafi bangaren jagoranci da zamantakewa da dalibai
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - Wata matashiya ‘yar asalin jihar Neja a Najeriya Hajara Yakubu Jibril, ta samu gagarumar nasara a fagen ilimi da shugabanci a ƙasar waje.
An karrama Hajara Yakubu da lambar yabo ta Dalibar Afirka Mafi Hazaka da ta kammala karatu a jami’ar Lovely Professional University (LPU) da ke jihar Punjab, Indiya.

Source: Getty Images
Hajara, wacce ‘yar asalin karamar hukumar Suleja ce a Jihar Neja, ta kammala karatun digiri na farko a fannin ilimin hada magunguna watau Pharmacy, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan
Ana hallaka jama'ansa, Gwamna Radda zai kashe Naira miliyan 680 a gyaran maƙabartu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta kammala karatu da sakamako mai daraja ta farko First Class a shekarar 2025, tana da shekaru 21 kacal.
Wannan bajinta ya sanya ta shiga sahun matasan Nijeriya da suka daukaka sunan ƙasar a fagen karatun boko a duniya.
Hajara Yakubu ta samu kyautattuka a India
Baya ga wannan babbar nasara, Hajara ta lashe wasu kyaututtuka da dama da suka haɗa da, Distinguished Leaders Award, Public Service Award da kuma Global Ambassador Award.
Hakan yana nufin ta yi fice, ta yi kokari wajen aiki sannan ta zama lambar jakadancin kwarai.
Wannan ya nuna cewa ba a ilimi kadai ta yi fice ba, har ma ta taka rawa wajen jagoranci da hidimar jama’a a tsakanin dalibai da suka zo daga kasashe daban-daban a jami'ar.
Tsohon shugaban ƙungiyar lauyoyi ta Nijeriya (NBA) reshen Suleja, Barista Idris Abdullahi, ya bayyana farin cikinsa kan wannan bajinta da Hajara ta yi.
A cewarsa, matashiyar ta sanya Nijeriya ta yi alfahari da ita, musamman a irin wannan lokaci da ake ta kira ga matasa da su rungumi gaskiya, himma da kishin ƙasa.
An nemi gwamnati ta karrama Hajara
Ya kuma yi kira ga gwamnati a matakin jiha da na tarayya da su karrama ta, domin ƙarfafa sauran matasa su yi koyi da jajircewarta.
“Ya kamata gwamnati ta ba da tallafi da yabo ga irin waɗannan matasa masu kwazo, domin hakan zai ƙarfafa sauran ɗalibai su tashi tsaye wajen yin aiki tukuru,” in ji shi.

Source: Original
Hajara ta kasance abin koyi ga dubban matasa, musamman ‘yan mata, domin ta nuna cewa babu abin da mace ba za ta iya cimmawa ba idan aka haɗa himma, tsari da dagewa da karatu.
Wannan nasara ta sake tabbatar da cewa matasan Nijeriya na iya fafatawa da takwarorinsu a ko ina cikin duniya idan aka ba su damar da ta dace.
Jami'ar OOU ta sanya wa mata doka
A wani labarin, kun ji cewa jami'ar Olabisi Onabanjo (OOU),) da ke jihar Ogun ta sanya ta dauki matakai domin gyara tarbiyyar dalibai mata a cikin makaranta.
Hukumar makarantar ta sanya dokar cewa ya zama wajibi kowace daliba ta rika sanya rigar mama, musamman a lokacin jarabawa.
Wannan doka dai ta jawo ce-ce-ku-ce daga yan Najeriya a sassa daban-daban, inda wasu ke ganin hakan ya dace yayin da wasu kuma ke ganin jami'ar ta tsaurara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

