Dalibi Ya Mayar Da Dakin Kwanansa Na Makaranta Karamin Kanti, Yana Ciniki Sosai

Dalibi Ya Mayar Da Dakin Kwanansa Na Makaranta Karamin Kanti, Yana Ciniki Sosai

  • Wata yar Najeriya ta cika da mamaki lokacin da ta ziyarci abokin karatunta a dakunan kwanan dalibai ta ga cewa ya mayar da nasa dakin karamin kanti
  • Da take wallafa bidiyon dakin matashin, budurwa ta nuno yadda aka shirya kayan siyarwar da kyau
  • Mutane da dama da suka yi martani ga bidiyon sun bayyana cewa lallai dalibin mai kwazo ne tunda ya iya hada kasuwanci da makaranta

Wata matashiya yar Najeriya, @sandraodfrey, ta garzaya soshiyal midiya don wallafa wani dan gajeren bidiyon abokin karatunta, Prosper wanda ya mayar da dakinsa dan karamin kanti.

Da take daukar bidiyon dakin matashin, budurwar ta nuno yadda aka yi wajenshirya kayayyaki dauke da abubuwa iri-iri.

Matashi da kanti
Dalibi Ya Mayar Da Dakin Kwanansa na Makaranta Karamin Kanti, Yana Ciniki Sosai Hoto: TikTok/@prospiloliveblog, @sandraodfrey
Asali: UGC

Dalibi ya mayar da dakinsa cibiyar kasuwanci

Ya cika dakin da kaya. Saman gadon baccinsa ne kawai babu kaya shimfide. Duk sauran wuraren na da abubuwan siyarwa.

Kara karanta wannan

Canjin Takardun Kudi: Kira Zuwa Ga Hukuma, Daga Dr Sani Rijiyar Lemo

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An gano matashin wanda shine mamallakin karamin kantin yana kula da kwastamomi ta tagar dakin nasa.

Kalli bidiyon a kasa:

Vivienne@2014n.k.love ta ce:

"Huum ba ku ji sunansa 'prosper' wato Wadata ba. za ka samu wadata dan uwana da izinin Allah zat ka duba baya ka dara wata rana."

tonyeking ya ce:

"Na so wannan, ajiye asusun bankinka, ina so na taimaki kasuwancinka."

Otentikmariam do ya ce:

"Allah ya kadarci daukakarsa wannan mafari ne za ka daukaka da sunan Yesu."

Joy Amy Festus ta ce:

"Awww Prosper mai neman na kai ne, gaye zai zama babban mutum kwanan nan."

Ivyluchi ya ce:

"Prosper na da kwazo sosai."

Shopwithkloe ya ce:

"A hankali ake farawa, kafin ka sani ya zama babban kantin siyar da kaua. Misalin fara da abun da kake da shi. Sannu da kokari."

Kara karanta wannan

Bidiyon Dirarriyar Amarya Mai Shekaru 57 da ke Nuna Yarinta, Ta Saka Jar Riga ta Amaren Zamani

Amarya ta ce bata yin auren a ranar jajiberin bikinsu da angonta

A wani labari na daban, wata amarya ta hau sama ta dire inda ta ce sam ta fasa auren angonta a ranar jajiberin bikinsu bayan ta karanta wasikar da wata matashiya ta kawo masa gida.

Amaryar dai ta gano bashi ya yi wa angon nata katutu a kai domin har banki na shirin kwace kadarorinsa amma kuma ya boye mata bai sanar da ita ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel