Yadda wata budurwa 'yar Najeriya ta samu wata gagarumar kyauta daga wajen mai kudin duniya Bill Gates

Yadda wata budurwa 'yar Najeriya ta samu wata gagarumar kyauta daga wajen mai kudin duniya Bill Gates

- Wata yar Najeriya ta samu kyauta ta musamman daga gidauniyar Bill and Melinda Gates ta shekarar 2020

- Hauwa Ojeifo, ta samu kyautar ne sakamakon gudumawar da take bayarwa wurin daidaiton jinsi bayan fuskantar cin zarafi ta da taba yi

- Matar ta samu jinjinar Queen's Young Leaders sakamakon lura da kokarinta wurin jawo masu matsalar kwakwalwa a jikinta da kuma basu kwarin guiwa

Wata 'yar Najeriya mai suna Hauwa Ojeifo ta samu gagarumar kyauta ta musamman daga gidauniyar Bill Gates da Melinda Gates ta shekarar 2020.

Kasancewar budurwar mai rajin kare hakkin jinsi da nakasassu ce, tana jagorantar wata kungiya mai taimako da bada shawarwari ga masu fama da rashin lafiyar kwakwalwa.

Hauwa Ojeifo tana bawa masu damuwa karfin gwuiwa ne ta hanyar basu labarin rayuwarta da irin kalubalen da ta fuskanta.

Yadda wata budurwa 'yar Najeriya ta samu wata gagarumar kyauta daga wajen mai kudin duniya Bill Gates
Bill Gates ya yiwa 'yar Najeriya gagarumar kyauta | Photo credit: Premium Times
Asali: UGC

KU KARANTA: Zargin hadin baki a kan rashin tsaron Zamfara: CNG ta mika korafi ga Buhari

Jaridar Legit.ng ta tattara bayanai daga gidauniyar a ranar Talata, 22 ga watan Satumba dake nuna yadda Hauwa tayi fice a ayyukan ta na daidaiton jinsi da taimakon masu matsalar kwakwalwa.

Ta samu jinjinar ne tun bayan kula da akayi da yadda take taimakon masu cutar tabin hankali kuma tana hana mutane kyamatar su.

Ta zama yar Najeriya ta farko da ta samu wannan gagarumar kyauta ta jinjina

Yadda wata budurwa 'yar Najeriya ta samu wata gagarumar kyauta daga wajen mai kudin duniya Bill Gates
Bill Gates ya yiwa 'yar Najeriya gagarumar kyauta | Photo credit: Premium Times
Asali: UGC

KU KARANTA: Fyade a Kano: 'Yan majalisa sun mika bukatar fara yi wa masu fyade dandatsa

Shi kuwa biloniyan dan kasuwa Charles Chuck Feeney a karshe dai ya cika burinshi na rayuwa, inda ya dinga addu'ar ya talauce tun yana da rai, a karshe dai hamshakin mai kudin ya bayar da dukiyarshi sadaka baki daya.

Mutumin wanda ya samar da kamfanin Duty Free Shoppers, ya ce akwai dadi sosai idan ka bayar da dukiyar ka tun kana raye ba wai sai ka mutu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel