Tashin Hankali: Ɗan Sanda Ya Saita Bindiga, Ya Harbe Soja har Lahira a Bauchi
- Wani dan sanda da ke aiki a sashen rundunar na MOPOL ya saita bindiga, ya harbe wani sojan Najeriya har lahira a jihar Bauchi
- An ce takaddama ta barke a lokacin da sojoji suka nemi duba wata motar kamfanin 'yan China da ke hakar ma'adanai a garin Futuk
- Rundunar sojojin Najeriya da rundunar 'yan sanda ta yi bayani game da matakin da aka dauka kan jami'in da ya yi harbin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi - Al'ummar garin Futuk da ke cikin karamar hukumar Alkaleri, jihar Bauchi sun shiga firigici a lokacin da wani dan sanda ya kashe soja.
An rahoto cewa wani dan sanda mai mukamin Sufeta a sashen 'yan sanda na MOPOL, ya saita bindiga, ya harbe sojan har lahira a Futuk.

Source: Getty Images
Rigimar sojoji da 'yan sanda a Bauchi

Kara karanta wannan
Abin da ya sa aka dauke sabis din MTN a Kano da wasu jihohi 2 a Arewacin Najeriya
Wani da abin ya faru a gaban idonsa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce dan sanda yana aiki ne da wani kamfanin 'yan China, inji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta ce dan sandan yana rakiyar wata babbar mota da ake zargin an makare ta da ma'adanai da kamfanin Chinan ya hako, lokacin da abin ya faru.
Ana zargin cewa kamfanin Chinan ya hako wadannan ma'adanai ne ba bisa ka'ida ba, a wani wajen hako ma'adanai da ke yankin Yalo.
Rigima ta tashi ne a daidai lokacin da dakarun sojoji da aka ajiye a shingen bincike na garin Futuk suka yi kokarin dakatar da motar.
'Dan sanda ya harbe soja har lahira
An ce shi direban motar ne ya ki bin umarnin sojojin, ya wuce shingen ba tare da ya tsaya ba, wanda ya sa sojojin suka bi bayan motar a ta su abin hawar.
A lokacin da suka cimma motar suka tsayar da ita, an ce cacar baki ta barke tsakanin sojoji da 'yan sandan da ke rakiyar wannan mota.
Ana cikin cacar bakin ne daya daga cikin 'yan sandan ya ciro bindiga, ya saita daya daga cikin sojojin, ya harbe shi nan take.
Majiyar ta ce an gaggauta daukar sojan da aka harba zuwa wani asibiti da ke cikin jihar Gombe, inda a nan ne aka tabbatar da mutuwarsa.
Abin da sojoji suka ce kan kisan jami'insu
Mukaddashin mataimakin darakta, sashen hulda da jama'a na rundunar sojoji ta 33, Manjo Atang Hallet Solomon, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Sai dai, Manjo Atang Solomon bai bayar da karin bayani game da lamarin ba, inda ya ce suna kan gudanar da bincike, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
"Muna da kyakkyawar alaka da rundunar 'yan sandan, kuma ana kan gudanar da bincike na hadin gwiwa domin gano bakin zaren lamarin."
- Manjo Atang Hallet Solomon.

Source: Twitter
'Yan sanda sun yi martani bayan kisan
Mukaddashin mataimakin daraktan ya ce ba zai iya bayar da bayani game da motar da abin da ke cikinta ba har sai an kammala bincike.
Ya kuma tabbatar da cewa direban motar ya tsere daga wurin da abin ya faru, kuma jami'in da ake zargin ya yi harbi yana tsare.
Da aka tuntubi jami'in yada labarai na rundunar 'yan sanda a Bauchi, SP Ahmad Wakili, ya ce an kwamishinan 'yan sandan jihar ya shirya kai ziyara wurin da abin ya faru.
"Kwamishinan zai ziyarci wurin da abin ya faru a ranar Alhamis. Za a fitar da karin bayani da zarar an samu cikakkun bayanai."
- SP Ahmad Wakili.
Soja ya harbe shugaban 'yan sanda
A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar yan sandan jihar Zamfara ta yi Allah wadai da kisan da ta zargi wani sojan Najeriya da yi wa jami'in dan sanda.
Kakakin yan sanda a jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar ya bayyana cewa an kashe dan sandan ne duk da ya nuna katin shaidar aiki.
Haka zalika ASP Yazid Abubakar ya yi kira na musamman ga hukumomi kan gaggauta bincike tare da daukar matakin da ya dace don bin kadin jinin jami'in.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

