Majalisar Musulmi a Taraba Ta Zafafa Hukunci a kan Masu 'Kauyawa Day' da Ajo
- Majalisar Musulmi a Taraba ta haramta dukkannin nau’ikan shagulgulan biki a Jalingo domin tsaftace al'umma
- Tuni limamai su ka fara gargadin Musulmi cewa za a fasa ɗaura auren duk wadanda aka samu da karya dokar
- Sauran hukunce-hukuncen sun haɗa da hana yi masu jana’iza ko kuma halartar suna a gidajensu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Taraba– Majalisar Musulmi ta jihar Taraba tare da goyon bayan sarakunan gargajiya da hukumomi ta sanar da dakatar da dukkanin nau’ikan shagulgulan aure a Jalingo.
Wannan ya haɗa da shagulgulan “Kauyawa Day” da “Ajo”, inda matasa kan taru da dare suna rawa da sunan nishadin bikin.

Source: Original
Daily Trust ta wallafa cewa wannan batu ya zama jigon hudubar limaman Juma’a a masallatan Jalingo a ranar Juma’ar da ta gabata.
An rika tunatar da jama'a cewa an sanya dokar ne domin a dawo da yakana da tarbiyya a tsakanin Musulmin jihar da kuma rage baɗala.
Majalisar Musulmi ta hana wasu shagulgula
Trust TV ta wallafa cewa limamin babban masallacin Mayo Gwoi, Imam Tajudeen Nuhu, ya bayyana cewa daga yanzu haramun ne a gudanar da shagulgula 'ajo' da 'kauyawa day'.
Imam Tajudeen Nuhu ya ce:
"Daga yau, ba a yarda kowane gida ya sake bikin ranar Kauyawa, Ajo, ko wani irin biki makamancin haka yayin aure a Jalingo.”
Majalisar ta kuma gargadi cewa duk Musulmin da ya saba wa wannan doka, ba za a daura auren gidansa ba idan biki ya taso.
Majalisar Musulmi ta fitar da hukuncin karya doka
Baya ga kin daurin aure, an kuma haramta wa malamai ko limamai yin sallar jana’iza a gidajen da suka saba wa wannan doka.
Haka kuma ba za a ba su damar zuwa halartar duk abin da ya shafi aure ko suna a irin waɗannan gidaje ba.

Kara karanta wannan
'Mun sha azaba,' Adadin bayin Allah da 'yan ta'adda su ka hallaka a Katsina ya haura 55

Source: Twitter
An kuma umarci duk wani malami ko limami cewa idan ya halarci jana’iza ko suna a gidan wanda ya karya doka, zai fuskanci hukunci.
Daga cikin matakan da za a ɗauka a kansa har da korar sa daga limancin masallaci.
Majalisar Musulmi ta Taraba ta ce manufar wannan mataki shi ne dawo da tarbiyya, tsoron Allah da kuma bin doka a cikin al’ummar Musulmi na Jalingo.
Haka kuma an yi kira ga Musulmi su yi biyayya domin kauce wa hukunci da kuma tabbatar da tsari cikin al’umma.
Dalilin haramta 'kauyawa day' a Kano
A baya, mun wallafa cewa hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta sanar da dakatar da duk wani biki da sunan 'Kauyawa Day' a fadin jihar.
Wannan na zuwa ne bayan sabon gyaran doka da majalisar dokoki ta jihar ta amince da shi a 2025, wanda gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya wa hannu.
A wata sanarwa da sakatare janar na hukumar, Abba El-Mustapha, ya fitar, ya ce an dauki matakin ne domin kare tarbiyya da tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
