'Yan Bindiga Sun Kashe Fiye da Mutum 10, Sun Raba Dubban Mutane da Gidajensu a Filato
- 'Yan bindiga da yawansu ya haura 1,000 sun kai farmaki kan garuruwan Chakfem, inda suka kashe mutane 12, ciki har da jariri
- An rahoto cewa maharan sun ƙona gidaje, sun lalata dukiya, sun sace dabbobi, sannan suka kashe mata, yara da kuma dattawa
- Wani shugaban matasa, Simon Takbang ya roƙi gwamnati ta girke jami’an tsaro, ta kuma taimaka masu wajen sake gina kauyukansu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Filato - Wani shugaban matasa a jihar Filato, Simon Takbang, ya bayyana yadda ‘yan bindiga suka kai hari kan garuruwan masarautar Chakfem da ke ƙaramar hukumar Mangu.
Simon Takbang ya labarta cewa mutane 12 aka kashe a wannan harin, sannan aka raba dubban mutanen garin da muhallansu a ranar Litinin.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun kashe mutane 12 a Filato
A ranar Juma'a, Takbang ya shaida wa manema labarai, ciki har da Punch cewa 'yan bindigar da yawansu ya haura mutane 1,000, sun afkawa kauyuka da dama a yankin, ciki har da Manden, Tim, Mhidihin, Jibin, Jiblang, Koppang, da Jilem.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban al'ummar, ya ce:
“Sun ƙona gidaje, sun lalata dukiyoyi, sun sace dabbobi, sannan suka kashe mutane 12 ciki har da mata da ƙananan yara.”
Shugaban ƙungiyar matasan Chakfem ya lissafa sunayen waɗanda aka kashe, da suka haɗa da jaririya ‘yar wata huɗu, Yilshwal Godwin, da kuma dattawa da yara da dama.
Daga cikin waɗanda suka mutu akwai: Rifkatu Katde (80), Talatu Joel (53), Tapmwan Benard (29), Danlami Kyenba (50), Maichibi Sonyen (81), Ishaku Yohana (26), da Joel Longpwen (62).
"Ana son raba mu da gidajenmu" - Takbang
Shugaban matasan ya nemi gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa domin kamo waɗanda suka aikata ta’asar tare da gurfanar da su a gaban shari’a.
Takbang ya ce:
“Waɗannan hare-hare ba na ta'addanci ne kawai ba, wata makarkashiya ce kawai aka shirya, don a kwace mana ƙasarmu ta gado, a raba mu da gidajenmu, tare da canza tsarin zamantakewarmu.”

Kara karanta wannan
'Mun sha azaba,' Adadin bayin Allah da 'yan ta'adda su ka hallaka a Katsina ya haura 55
Ya ce duk da raɗaɗin da suke ciki, dole su yaba da yadda gwamnati ta aika jami’an tsaro cikin gaggawa domin dakile harin, da kuma taimakon kayan tallafi da aka rarraba.
“Wannan ya tabbatar mana cewa gwamnati na tare da mu, ba a bar mu mu ƙaɗai cikin wannan mawuyacin hali ba,” inji Takbang.

Source: Original
Rokon 'yan Filato ga gwamnati kan tsaro
Shugaban matasan ya kuma roƙi gwamnati da ta girke jami’an tsaro na dindindin a yankunansu da kuma tallafa musu wajen sake gina kauyukan da aka lalata.
Takbang ya ce:
“Yana da matuƙar muhimmanci a girke jami'an tsaro, saboda yanayin ƙasarmu ba ya ba jami'an tsaro daga nesa damar kai daukin gaggawa idan an kai mana hari.
"Saboda haka akwai buƙatar a gaggauta gudanar da aikin titunan Chakfem domin sauƙaƙa zirga-zirga da kuma shigowar jami’an tsaro a irin waɗannan lokuta.”
Ya kuma buƙaci gwamnati ta haɗa kai da kamfanonin sadarwa domin ƙarfafa hanyoyin sadarwa a yankin, saboda hakan zai sauƙaƙa kiran agaji da sadarwa a lokutan hare-hare.
'Yan bindiga sun kashe mutane a Mangu
Tun da fari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai hari garin Tim, da ke masarautar Chakfem a karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun yi ta'asa a Plateau, an kashe mutane tare da bankawa gidaje wuta
'Yan bindigan sun kashe mutane biyar tare da kone gidaje guda 10 a yayin wannan mummunan harin da suka kai.
Majiyoyi daga garin sun tabbatar da cewa an riga an kwashe gawarwakin waɗanda aka kashe domin yi musu jana’iza, yayin da waɗanda suka samu raunuka ke kwance a asibitoci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
