Fadar Shugaban Kasa Ta Ragargaji Atiku, El Rufa'i kan Wata Nasarar da Tinubu Ya Samu

Fadar Shugaban Kasa Ta Ragargaji Atiku, El Rufa'i kan Wata Nasarar da Tinubu Ya Samu

  • Fadar shugaban ƙasa ta yi ba’a ga Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai da Babachir Lawal bayan asusu ajiyar wajen Najeriya ya karu
  • Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce wannan nasara ta samu ne ba tare da Najeriya ta dogara da kuɗin man fetur ba
  • Ya ce wannan ci gaban ya kasance karo na farko cikin shekaru huɗu da Najeriya ta samu wannan matsayi tun daga shekarar 2021

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Fadar shugaban ƙasa ta yi ba’a ga manyan ‘yan adawa ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi.

Haka zalika ta hada da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da kuma tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal.

Kara karanta wannan

Nijar: An harbe shugaban Boko Haram da ya maye gurbin Shekau har lahira

'Yan adawan Najeriya tare da shugaba Tinubu
'Yan adawan Najeriya tare da shugaba Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga|Atiku Abubakar|Peter Obi
Source: Twitter

Bayo Onanuga ne ya yi maganar a wani sako da ya wallafa a X bayan an bayyana cewa asusun wajen Najeriya ya kai Dala biliyan 41.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakin ya zo ne a lokacin da waɗannan jagororin siyasa suke ci gaba da adawa da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu karkashin tutar ADC, wacce ke ƙoƙarin kwace mulki a zaben 2027.

Bayo Onanuga ya ce wannan nasarar alama ce ta kyakkyawan tafiyar da tattalin arziƙin ƙasa karkashin Tinubu.

Nasarar da gwamnati ke murna da ita

Onanuga ya bayyana cewa wannan ci gaban bai samo asali daga karuwar kuɗin shigo da man fetur ba, domin a yanzu farashin mai a kasuwannin duniya na ci gaba da sauka.

Ya ce:

“Wannan nasara ta faru ne saboda kyakkyawan tsarin tafiyar da tattalin arziƙi da shugaba Bola Tinubu ya bullo da shi.
"Ina tabbatar da cewa Atiku, Obi, El-Rufai da Babachir ba za su taɓa yarda da wannan ci gaban ba, domin sun fi mayar da hankali wajen ƙoƙarin hambarar da gwamnati.”

Kara karanta wannan

Zaben 2027: An gano yadda ake amfani da siyasa wajen zafafa hare hare a Najeriya

Adawar siyasa da suka ga Tinubu

Jagororin adawan sun dade suna sukar matakan gwamnati musamman na ɓangaren tattalin arziƙi, suna cewa har yanzu ba a ga tasirin sauye-sauyen da ake ikirari a kai ba.

Sai dai fadar shugaban ƙasa na ganin cewa wannan ci gaba ya isa hujja ta gaskiya wacce ke tabbatar da cewa ana samun sauyi a fannin tattalin arziƙi.

Jagororin 'yan adawa a wani taro a Abuja
Jagororin 'yan adawa a wani taro a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Yadda asusun kudin wajen Najeriya ya karu

Rahoton tashar Arise ya nuna cewa kudin asusun wajen ya tashi daga $40.3bn zuwa fiye da $41bn, wanda hakan shi ne karo na farko tun shekarar 2021.

Fadar shugaban kasa na ganin wannan alama ce da ke nuna ƙasar na komawa kan turba, duk da cewa akwai ƙalubale a bangaren kuɗin shiga da farashin kayayyaki.

Sai dai har yanzu manyan ‘yan adawa da aka caccaka ba su bayyana matsayinsu kan wannan batu ba.

Tinubu ya kawo manhajar lissafa haraji

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da manhajar lissafa haraji.

Kara karanta wannan

Adamawa: An kama matar da ke sace yara daga Arewa zuwa Kudu ta sayar da su

An kawo na'urar ne domin ba dukkan 'yan Najeriya damar sanin yadda sababbin dokokin haraji za su shafe su.

Shugaba Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya da su gwada aiki da manhajar domin sanin harajin da za su fara biya daga 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng