Nijar: An Harbe Shugaban Boko Haram da Ya Maye Gurbin Shekau har Lahira
- Sojojin Nijar sun sanar da kashe shahararren kwamandan Boko Haram, Ibrahim Mahamadu (Bakura) da aka daɗe ana nema
- An ce an hallaka shi ne a wani samamen jirgin yaki da aka kai kan tsibirin Shilawa a yankin Diffa ranar 15 ga watan Agusta
- Bakura ya kasance ɗaya daga cikin manyan magoya bayan Abubakar Shekau, wanda ya ƙi shiga ɓangaren ISWAP tun 2021
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nijar– Rundunar sojin ƙasar Nijar ta tabbatar da cewa ta yi nasarar kashe Ibrahim Mahamadu, wanda aka fi sani da Bakura, babban kwamandan Boko Haram a yankin Tafkin Chadi.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, an bayyana cewa an kaddamar da wannan farmaki ne ta sama a ranar 15 ga watan Agusta 2025.

Source: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa jiragen yaki ne suka kai hare-hare uku a jere kan matsugunan da Bakura ke amfani da su a tsibirin Shilawa na Diffa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya zo ne bayan shekaru da dama ana fafutukar ganin an kawo ƙarshen aikata miyagun ayyukan sa a cikin yankunan da Boko Haram ke addabar rayuwar al’umma.
Yadda aka kashe shugaban Boko Haram
Sojojin sun bayyana cewa sun kai farmaki ne da ya yi sanadiyyar mutuwar Bakura, wanda aka bayyana a matsayin “babban jagoran da ake tsoro.”
A cewar rundunar, hare-haren da aka kai da sanyin safiyar ranar 15 ga watan Agusta sun hallaka Bakura tare da tarwatsa maboyar mayaƙansa a yankin.
Bakura ya shahara da kai hare-hare a yankin Diffa tun bayan mutuwar Abubakar Shekau, inda ya ƙi haɗuwa da bangaren ISWAP, ya koma tsibirai da mayaƙansa a bangaren Nijar na Tafkin Chadi.

Source: UGC
Tarihin Bakura a kungiyar Boko Haram
Punch ta wallafa cewa Nijar ta ce Bakura, dan asalin Najeriya ne mai kusan shekara 40, kuma ya shiga cikin Boko Haram sama da shekaru 13 da suka gabata.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun yi ta'asa a Plateau, an kashe mutane tare da bankawa gidaje wuta
Bayan mutuwar Shekau a cikin rikicin cikin gida a tsakanin 'yan ta'adda a 2021, Bakura ne ya karɓi ragamar wannan ɓangaren da ya ci gaba da kai hare-hare a yankunan Najeriya da Nijar.
Shugaban ƙasar Nijar, Janar Abdurahamane Tchiani ya bayyana Bakura a matsayin ɗaya daga cikin manyan mutanen da ke ƙoƙarin tayar da hankula da lalata tsaron ƙasar.
Rikicin yakin Boko Haram da tasirinsa
Tun daga 2009, rikicin Boko Haram ya fara a Arewa maso Gabashin Najeriya, inda ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 40,000 tare da raba fiye da mutane miliyan 2 da gidajensu.
Har ila yau, rikicin ya wuce kan iyaka, inda Nijar ta fara dandana hare-haren Boko Haram tun a Bosso a 2015, a gefen Tafkin Chadi.
Sojoji sun kama makamai a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar kama makamai a karamar hukumar Nafada da ke Gombe.
Rahotanni sun bayyana cewa an dauko makaman ne daga jihar Borno ana shirin tafiya da su Arewa maso Yamma.
Binciken da aka fara sun nuna cewa ana zargin wani soja a jihar Yobe da alaka da makaman kuma tuni aka fara neman shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
