Wata Sabuwa: Hafsan Tsaro Ya Bar Boye Boye, Ya Fadi Masu Kawo Tsaiko a Najeriya

Wata Sabuwa: Hafsan Tsaro Ya Bar Boye Boye, Ya Fadi Masu Kawo Tsaiko a Najeriya

  • Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce bakin da ke shigowa suna kara ta’azzarar matsalar tsaro musamman a iyakokin kasar
  • Babban jami'in tsaron ya bayyana cewa ana sayen makamai cikin sauki a iyakoki, yana mai kira a dauki matakai domin kare Najeriya
  • Janar Musa ya ce kungiyoyin Boko Haram da Lakurawa sun samu karfi ne bayan an bar su shiga kasar tun farko ba tare da tsangwama ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya yi magana kan matsalar tsaro da ake fama da shi.

Jamar Musa ya bayyana dalilan da suka saka ake samun shigowar baki Najeriya wanda ke kara ta'azzara tsaro.

Hafsan tsaro ya fadi abubuwan da ke kara rashin tsaro
Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa yayn taron jami'an tsaro a Abuja. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Hafsan tsaro ya bude aiki kan matsalar tsaro

Hafsan tsaron ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a daren yau Alhamis 21 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan

Tsohon ministan Buhari ya yi magana game da mulki, 'yan adawa da halin da APC take ciki

Janar Musa ya ce baki da ke shigowa kasar suna taka rawa wurin kara rashin tsaro ta iyakokin kasar baki daya.

Ya ce:

"Maganar masu daukar nauyin ta'addanci akwai su amma ba zan iya saninsu ba saboda ba layi na ba ne, amma ministan shari'a yana aiki a kai.
"An fara hukunta wasu, ina da tabbacin ka san wadanda suka kai harin bam a yanzu haka ana tuhumarsu.
"Ka san an samu matsala a Libya, sannan ga rashin tsaro a Burkina Faso da yankin Sahel gaba daya hakan matsala ne."

Hafsan tsaro ya ce ana samun matsala musamman a bakin iyakokin Najeriya wanda ke kara matsalar tsaro.

Ya bukaci daukar matakai domin dakile masu yawan shigowa daga ketare domin kare Najeriya daga matsalolin tsaro.

Ya kara da cewa:

"Sabosa bakin iyaka sai a hankali ana sayan makamai babu kakkautawa, kowa burinsa shi ne ya shiga Najeriya.
"Saboda suna ganin Najeriya tana da arziki ga girma kuma wani abu da ya kara hakan shi ne yan Najeriya suna da saukin kai da tausayi.

Kara karanta wannan

'An san wadanda suka shiga masallaci, suka kashe masu sallah a jihar Katsina'

"Duk da haka dole mu kula da tsaronmu, wani lokacin wadannan mutane za su shiga sai mu ce ai yan uwanmu ne."
Hafsan tsaro ya fadi abubuwan da ke kara matsalar a Najeriya
Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar yayin jawabi ga manema labarai. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Janar Musa ya magantu kan Boko Haram, Lakurawa

Har ila yau, Janar Musa ya bayyana farkon yadda aka samu matsala tun shigowar Boko Haram da Lakurawa.

'Wannan shi ne matsalar, haka muka bar Lakurawa da Boka Haram suka shigo har suka yi karfi daga baya muka fara korafi.
"Bai kamata mu bar wani dan kasar waje ya shigo Najeriya ba ko da taku daya, kowane irin dalili zai kawo shi."

- Cewar Janar Musa

Sojoji sun babbake 'yan bindiga a Zamfara

Kun ji cewa sojojin Najeriya sun gano gawarwakin 'yan bindiga fiye da 60 bayan luguden wuta kansu a Zamfara da ake kukan rashin tsaro.

Sama da babura 30 da makamai sun kone, fiye da ‘yan ta’adda 100 sun mutu a harin da aka kai wanda ya kara rikita yan ta'addan a yankin.

Rundunar ta ci gaba da farautar maboyarsu domin hana sake haduwa ko kai hari a cikin dazukan yankin da ke fama da matsalolin tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.