'An San Wadanda Suka Shiga Masallaci, Suka Kashe Masu Sallah a Jihar Katsina'

'An San Wadanda Suka Shiga Masallaci, Suka Kashe Masu Sallah a Jihar Katsina'

  • Dan majalisar wakilai daga Katsina, Hon. Sada Soli Jibia ya yi ikirarin cewa an san yan bindigar da suka kashe masallata akalla 30
  • Sada Soli ya bayyana cewa yan bindigar da suka yi wannan aika aika su na rike da wani yanki a jihar Katsina da ake yawan ta'adi
  • Sai dai ya ce gwamnatin Katsina kadai ba za ta iya magance matsalar tsaron jihar ba, ya na mai kira ga Gwamnatin Tarayya ta kai dauki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Hon Sada Soli, mamba mai wakiltar Jibia/Kaita a majalisar wakilai ya bayyana cewa ’yan bindigar da suka kashe masallata a Katsina na rike da wani yanki.

Sada Soli ya yi ikirarin cewa akwai yankin da ke karkashin ikon 'yan bindigar da suka shiga masallaci, suka kashe masu sallah a yankin karamar hukumar Malumfashi.

Kara karanta wannan

Da gaske an yi wa Sheikh Jingir ihu a Abuja? Izala ta fadi abin da ya faru

Dan majalisar tarayya, Hon. Sada Soli Jibia.
Hoton dan Majalisar Wakilai, Hon. Sada Soli Jibia a wurin wani taro a mazabarsa da ke Katsina Hoto: Hon. Sada Soli Jibia
Source: Facebook

Dan Majalisar ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV a ranar Laraba.

'Yan bindiga sun kashe masu sallah

Idan baku manta ba wasu yan bindiga sun rutsa mutane a cikin masallaci ana tsakiyar sallar subahi a kauyen Unguwar Mantau, inda suka kashe akalla mutum 30.

Gwamnatin Katsina ta tabbatar da aukuwar lamarin, kuma ta sha alwashin ci gaba da kokarin kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Ana zargin 'yan bindiga sun kwace yanki

Da yake magana kan yan bindigar da suka kai harin, Hon. Sada Soli ya ce:

"Su ne ke rike da wasu yankuna a cikin jihar, babu mai iko a wurin sai su. An san Yan bindigar nan musamman a yankin Kankara da ke iyaka da jihar Zamfara.
"Suna shiga Kankara, daga nan sai su shiga Malumfashi, daga nan kuma su shiga Funto a daya ɓangaren. Waɗannan duk ƙananan hukumomi ne da suke da iyaka da juna, kuma hakan na kawo matsaloli.”

Kara karanta wannan

Bayan korafe korafe, Tinubu ya dauki alƙawari bayan kisan masallata a Katsina

Ɗan majalisar ya ce ’yan bindigar sun daɗe suna addabar yankin, musamman sakamakon tasirin rikici da matsalar tsaron da ke jihar Zamfara.

“Babban matsalar mu a Katsina ita ce rikicin da ke faruwa a Zamfara," in ji Sada Soli.

Da gaske an san yan bindigar da suka kashe masallata?

Game da batun ko an san waɗannan ’yan bindigar, Hon Aada Soli ya ce:

"Ba wai daga sama suke sauka ba, mutane ne da ke zaune tare da mu. Ba wai daga wani wuri suke zuwa ba, jami’an tsaro ma sun san su.”

Sai dai ya jaddada cewa, matsalar tsaron da ake fama da ita a wasu sassan jihar ta fi karfin gwamnatin Katsina kadai, in ji rahoton Punch.

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda.
Hoton gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda a cikin gidan gwamnati Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Dan Majalisar ya ce gwammatin Katsina kadai ba za ta iya dawo da zaman lafiya ba, ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta shiga cikin lamarin domin kawo karshen matsalar.

Wani mazaunin Katsina a daya daga cikin yankunan da ke fama da matsalar tsaro ya shaida mana cewa akwai bukatar tashi tsaye kan yan bindiga.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Hafsan tsaro ya bar boye boye, ya fadi masu kawo tsaiko a Najeriya

Matashin mai suna Auwalu a takaice, wanda ya nemi kada a fadi cikakken sunansa ya fadawa wakilin Legit Hausa cewa a bayyane take gwamnati ta gaza.

Ya ce:

"Ba sai mun je ko'ina ba, kowa ya san gwamnati ta gaza kan tsaro, wannan abin da ya faru a Malumfashi kadan ne daga cikin barnar da barayin daji ke mana a Katsina.
"Mu dai yanzu a yankinmu mun dauki matakin kare kanmu, na fi yarda na mutu wajen kare iyalai da yan uwana musulmi da a zo har gida a kashe ni.
"Muna fatan gwamnati za ta bullo da dabarun magance wannan matsalar, gwamnanmu yayi kokari sosai amma har yanzu tsaron Katsina kara tabarbarewa yake."

Yan bindiga sun kashe kansu a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa fada ya barke tsakanin dabar ‘yan bindiga a jihar Katsina inda suka yi musayar wuta yayin da ake maganar sulhu a wasu yankuna.

Wannan rigima ba ita ce karon farko ba da ake samu tsakanin manyan yan bindiga wanda ke ragewa jami'an tsaro aiki a yaki da ta'addanci.

Shaidu sun ce fadan ya kaure tsakanin dabar da Samaila daga kauyen Salihawa ke jagoranta da kuma wata dabar Muhammadu daga kauyen Maharba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262