Kotu Ta Rufe Asusun Banki 4 da ake Zargin na da Alaka da Tsohon Shugaban NNPCL, Kyari

Kotu Ta Rufe Asusun Banki 4 da ake Zargin na da Alaka da Tsohon Shugaban NNPCL, Kyari

  • Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarni na wucin gadi a rufe asusun banki guda huɗu da aka danganta da tsohon Shugaban NNPCL, Mele Kyari
  • Hukumar EFCC ta ce bincike ya nuna cewa akalla N661.4m da ake zargin kudin da aka samo ta hanyar da ba ta dace ba ne, aka ajiye a cikin waɗannan asusun
  • Hukumar ta ce kuɗin sun fito ne daga NNPCL da wasu kamfanonin mai, a karkashin sunan tallafi da gudummawar wallafa wani littafi da kungiyar sa kai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja –Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin wuci gadi na a rufe wasu asusun bankuna hudu da ake alakanta wa da Mele Kyari.

Kara karanta wannan

Kudin data, kira za su yi sauki, Tinubu ya dakatar da harajin 5% na kamfanonin sadarwa

Wannan ya biyo karar da hukumar EFCC ta shigar gabanta kan zargin da Guardians of Democracy and Rule of Law ta mika mata na zargin tsohon Shugaban NNPCL da sata.

Tsohon Shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari
Mele Kyari a lokacin da ya ke jawabi ga wani taro a Abuja Hoto: NNPC Limited
Source: Facebook

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa EFCC ta shigar da wannan ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/1641/2025 tun ranar 11 ga watan Agusta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta sa an rufe asusun Mele Kyari

Vanguard ta wallafa cewa Mai shari’a Emeka Nwite ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, bayan lauyan EFCC, Ogechi Ujam, ya shigar da bukatar gaggawa a gaban kotun.

Kotun ta amince da roƙon ne bayan EFCC ta bayyana cewa asusun guda hudu na bankin Ja'iz na ƙarƙashin bincike saboda zargin tara kudin haram a cikinsu.

Mai shari’a Nwite ya dage sauraron ƙarar zuwa 23 ga watan Satumba domin samun rahoton ci gaban binciken da ake yi kan tsohon Shugaban NNPCL.

Tuhumar da EFCC take yi wa Kyari

A cewar hukumar EFCC, asusun da ta ke bincike sun haɗa da wanda ake buɗe da sunan Mele Kyari da kuma guda biyu na ƙungiyar Guwori Community Development Foundation.

Binciken farko ya nuna cewa an samu shigar kuɗI sama da N661.4m da ake zargin sun fito daga NNPCL da wasu kamfanonin mai.

Kara karanta wannan

Alhaki ya kama su: 'Yan bindiga sun yi hadari bayan karbo makudan kudin fansa

EFCC ta yi zargin cewa an aika kudin da sunan gudummawa domin taron ƙaddamar da littafi da kuma tallafa wa gidauniyar Guwori.

Shugaban hukumar EFCC, Ola OluKayode
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukayode Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Source: Facebook

EFCC ta ce Kyari ya rika sarrafa asusun ta hannun wasu ‘yan uwa da suke aiki a matsayin cewa asusun na su ne, alhali ba haka ba ne.

Martanin Kyari kan binciken EFCC

Kyari, wanda ya sauka daga kujarar Shugabancin NNPCL a watan Afrilu bayan gwamnatin Tinubu ta rushe shugabancin kamfanin, ya sha musanta zarge-zargen da ake yi masa.

A baya ya bayyana cewa labarin cewa an kama shi kan zargin satar $2.9bn don gyaran matatun mai ba gaskiya ba ne.

Ya ce:

“Na jagoranci NNPCL da tsoron Allah, kuma zan yi bayani a gaban Allah.”

EFCC: Mele Kyari ya musanta kama shi

A baya, mun wallafa cewa tsohon Shugaban NNPCL, Mele Kyari, ya musanta rahotannin da da ke bayyana cewa hukumar EFCC ta kama shi sannan ta tsare shi kan zargin zamba.

A sanarwar da Kyari ya fitar da kansa, ya bayyana cewa tun bayan ya sauka daga mukaminsa na jagorancin kamfanin mai na kasa, NNPCL ya ke hutu, amma ba a hannun EFCC ba.

Ya kara da cewa ya yi aiki na dogon lokaci da tsoron Allah da gaskiya, ya shafe shekaru 34 yana aiki a NNPCL, sannan ya shafe akalla shekaru shida a matsayin Shugaban kamfanin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng