An Saki Hotunan Bam da 'Yan Sanda Suka Gano a cikin Gonar Wani Manomi a Borno
- Al’ummar garin Dikwa da ke jihar Borno sun shiga firgici bayan wani manomi Babagana Kachalla ya gano bam a cikin gonarsa
- Kwamishinan ’yan sandan Borno, Naziru Abdulmajid, ya tura jami’an EOD zuwa gonar, inda suka kwance bam din cikin dabaru
- Bayan nasarar kwance bam ɗin, ’yan sanda sun yi wa mazauna bita kan illolin abubuwan fashewa da hanyoyin kare kansu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Al'ummar karamar hukumar Dikwa da ke jihar Borno sun shiga cikin firgici bayan da wani manomi ya gano wani abin fashewa a cikin gonarsa.
Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta ce jami'anta sun garzaya gonar, inda suka tarar da bam din da bai riga ya tashi ba a cikin gonar.

Source: Twitter
Manomi ya ga bam a gonarsa a Borno
'Yan sanda sun fitar da sanarwa game da yadda aka gano bam din da abin da ya biyo baya ta bakin kakakinsu, Nuhum Daso, a cewar rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar Nuhum Daso ta ce jami'an 'yan sanda sun gano bam din tare da kwance shi bayan manomin, Babagana Kachalla ya kai masu rahoto.
Babagana Kachalla ya garzaya wajen 'yan sandan ta gudunsa, inda ya sanar masu cewa ya ga wani abu da bai gamsu da shi ba a cikin gonarsa.
Bayan samun rahoton, Nuhum Daso ya ce kwamishinan 'yan sanda na Borno, Naziru Abdulmajid, ya tura jami'an kwance bam zuwa gonar Babagana.
Jami'an 'yan sanda sun kwance bam din
Sanarwar ta ce:
"An gano wannan bam din ne bayan da wani Babagana Kachalla ya kawo rahoton cewa ya ga wani abu da bai yarda da shi ba a cikin gonarsa.
"Bayan samun wannan rahoto, kwamishinan 'yan sanda na jihar Borno, CP Naziru Abdulmajid ya tura shugaban sashen kwance bam (EOD) na ofishin rundunar da ke Maiduguri.
"Kwamandan EOD da tawagarsa sun isa gonar Babagana Kachalla, kuma sun yi amfani da matakan EOD-CBRN wajen kwance wannan bam.
"Jami'an EOD din sun gudanar da abin da ake kira IN-SITU, watakan yi wa bam din dai-dai, kafin daga bisani su cire abubuwan fashewar."
Borno: An yi wa mutane bita kan bam
Sanarwar kakakin rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa jami'an sashen EOD sun yi nasarar kwance bam din ba tare da wata matsala ba
"An yi wa mutane bita kan hatsarin da ke tattare da abubuwan fashewa (EORA), wanda ya kara masu ilimi game da matakan da za su dauka idan sun gano ababen fashewar."
- Nuhum Daso.
Wasu hotuna da aka saki, sun nuna wannan bam din da aka gano a cikin gona, yayin da jami'an 'yan sanda ke kokarin kwance shi.
Kalli hotunan a kasa:

Source: Twitter

Source: Twitter
Bam ya kashe mutane 2 a Borno
Tun da fari, mun ruwaito cewa, wani bam da aka dauko daga bayan gari bisa rashin sani ya tarwatse a yankin karamar hukumar Konduga ta jihar Borno.
An tattaro cewa wasu yara su shida da ke harkar gwangwan ne suka dauko bama-bamai ba tare da sani ba, a tunaninsu karafa ne da za su sayar su samu kudi.
To sai dai kuma, yaran su na kan hanyarsu ta zuwa Ajari, wani kauye a cikin ƙaramar hukumar, lokacin da ɗaya daga cikin bama-baman ya fashe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

