Da Dumi-Duminsa: Jami'an Ƴan Sanda Sun Kwance Bam a Kano

Da Dumi-Duminsa: Jami'an Ƴan Sanda Sun Kwance Bam a Kano

- Jami'an yan sanda a jihar Kano sun yi nasarar kwance bam a kauyen Aujirawa a yau Juma'a

- Kakakin rundunar yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna ya tabbatar da lamarin

- Rundunar ta shawarci jama'a su rika saka idanu kan mutanen da ke kai-kawo a unguwanninsu

'Yan sanda a jihar Kano a ranar Juma'a sun kwance wani bam a ƙauyen Aujirawa da ke ƙaramar hukumar Gazawa a jihar kamar yadda TVC ta ruwaito.

Kwamishinan yan sanda, Isma'ila Dikko ya tabbatar da hakan cikin sanarwar da Kakakin yan sandan jihar DSP Abdullahi Haruna ya fitar a Kano.

DUBA WANNAN: Jerin Jihohi 10 da Suka Fi Arziki a Nigeria a Shekarar 2021

Da Dumi-Duminsa: Jami'an Ƴan Sanda Sun Kwance Bam a Kano
Da Dumi-Duminsa: Jami'an Ƴan Sanda Sun Kwance Bam a Kano. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

Mr Dikko ya ce an sanar da rundunar cewa an gano wani abu da ake zargin bam ne a garin.

Ya ce rundunar ta aike da jamianta na sashin kwance abin fashewa, EOD, wanda suka killace wurin kafin suka kwance bam din.

"Kwamishinan ya umurci tawagar masu kwance bam din karkashin jagorancin CSP Haruna Isma'il su tafi wurin da abin ya faru.

KU KARANTA: Raba Gardama: Gwamnatin Kwara Ta Ce Dalibai Musulmi Na Iya Saka Hijabi a Dukkan Makarantunta

"Bayan killace wurin, tawagar ta gano abin fashewar kuma ta yi nasarar kwance shi ta hanyar amfani da na'urarori.

"An fara bincike a kan lamarin," a cewar sanarwar.

Yayin da ya ke bawa mazauna garin shawarar su rika kula da abinda ke faruwa a kusa da su, Dikko ya bukaci su rika bada rahoto kan duk wani mutumin da ba su yarda da shi ba.

A wani rahoton, kun ji Rundunar yan sandan jihar Sokoto, a ranar Alhamis, ta ce ta kama a kalla mutane 17 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuka a jihar.

Mr Kamaldeen Okunlola, kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanarwar manema labarai hakan a Sokoto, Vanguard ta ruwaito.

Okunlola ya ce rundunar a ranar 4 ga watan Maris ta kama wani Jabbi Wanto kan hadin baki da sace mutane biyu a Tamba Garka a karamar hukumar Wurno na jihar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel