Mutane 62 da Aka Yi Garkuwa da Su Sun Tsero daga Hannun 'Yan Bindiga a Katsina
- Rundunar sojin saman Najeriya ta kai farmaki sansanin ɗan bindiga Muhammadu Fulani a karamar hukumar Danmusa, jihar Katsina
- Gwamnatin Katsina ta ce wannan farmakin ya ba wasu mutane 62 da aka yi garkuwa da su damar tserowa daga sansanin 'yan bindigar
- Gwamna Dikko Radda ya yaba da jarumtar jami’an tsaro, ya kuma ce gwamnatinsa ba za ta daina yaƙar ta’addanci ba har sai an samu tsaro
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina – Rundunar sojin saman Najeriya ta kai mummunan farmaki a sansanin fitaccen ɗan bindiga a ƙaramar hukumar Danmusa, jihar Katsina.
Wannan farmaki da sojojin saman suka kai ne aka ce ya ba wasu mutane 62 da aka yi garkuwa da su damar tserewa daga sansanin 'yan bindigar.

Source: UGC
Katsina: Sojoji sun farmaki sansanin 'yan bindiga

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Yan bindiga sun kutsa gidan Sarki da tsakar dare, sun sace ƴaƴansa
Jaridar Leadership ta rahoto cewa sansanin da ke Jigawa Sawai, shi ne maboyar jagoran kungiyar ’yan bindiga da aka fi sani da Muhammadu Fulani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya ce Muhammadu Fulani ya dade yana addabar garuruwan Matazu, Kankia, Dutsinma da ke Katsina da kuma wasu sassan jihar Kano.
Sojoji sun kai harin ne da misalin ƙarfe 5:10 na yammacin ranar Asabar, lamarin da ya tilasta ’yan fashin tserewa daga maboyarsu, tare da ba wadanda aka sace damar tserewa.
Mutane 62 sun tsero daga hannun 'yan bindiga
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Katsina, Dakta Nasir Mu’azu, ya sanar da cewa waɗanda aka yi garkuwa da su sun bayyana cewa kusan mutum 62 ne suka samu damar tserewa inda kowa ya yi ta kansa bayan guduwar ’yan bindigar.
Ya bayyana cewa mafi yawan waɗanda suka kubuta an sace su ne daga garin Sayaya yayin wani hari da ’yan bindigar suka kai a daren Litinin, 11 ga Agusta, 2025.
Dakta Mu’azu ya ƙara da cewa a halin yanzu, mutum 12 daga cikin waɗanda suka tsero na karɓar kulawar lafiya a asibitin gwamnati da ke Matazu.
Ya kuma ce wasu 16 na a sansanin sojoji na Army FOB a Kaiga Malamai inda suke samun kulawar farko da kuma daukar bayanansu don ci gaba da bincike.

Source: Facebook
Radda ya sha alwashi kan matsalar tsaro
Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar wa wadannan mutane cewa za a haɗa su da iyalansu bayan kammala duk gwaje-gwajen lafiya da ake bukata, inji rahoton Punch.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya yaba da jarumtar jami’an tsaro tare da sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta daina yaƙar ta’addanci ba har sai an kawo ƙarshen matsalar a jihar.
A matsayin wani mataki na dawo da zaman lafiya, gwamnati ta tura dakarun kai daukin gaggawa na QRW na rundunar sojin sama a yankin domin tabbatar da tsaro.
Dakta Mu’azu ya ƙara da cewa dakarun sojoji na ci gaba da sa ido kan lamarin domin ƙarin aikin ceto, kuma an samu tsaro sosai a yankin a yanzu.
Matsayar Radda kan sulhu da 'yan bindiga
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta zauna tattaunar sulhu da ƴan bindiga ba.
Sai dai gwamnan ya ce ƙofarsa a buɗe take na taimakon rayuwar ƴan ta'addan da suka amince za su ajiye makamansu, kuma su yi tuba na gaskiya.
Malam Dikko ya kuma yabawa ƴan sanda, sojojin sama da na ƙasa, dakarun hukumar NSCDC da jami'an tsaron da ya kirkiro bisa ƙoƙarin da suke yi a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

