Mata 6 da kananan yara 9 sun tsero daga hannun Boko Haram

Mata 6 da kananan yara 9 sun tsero daga hannun Boko Haram

  • Mutum 15 da suka hada da mata tare da kananan yara ne suka tsero daga hannun Boko Haram a Borno
  • Mata shida da kananan yara 9 an sace su ne daga jihohin Borno da kuma Adamawa yayin da suke gonakinsu
  • Kamar yadda gajiyayyun mutum 15 din suka bayyana, sun kwashe kwanaki shida suna tafiya a daji kafin su isa Damboa

Borno - Mata shida tare da yara kanana 9 da aka sace a yankin arewa maso gabas sun tsero daga hannun miyagun da suka sace su. Sun kwashe kwanaki shida suna tafiya a daji kafin su samu 'yanci a ranar Litinin.

Mutum 15 din an sace su daban-daban ne a gonakinsu da ke kauyukan Takulashi a Chibok , jihar Borno da kuma Cofure da ke karamar hukumar Hong ta jihar Adamawa watanni da yawa da suka gabata, Channels TV ta wallafa.

Kara karanta wannan

Kaduna: Jami'an tsaro sun halaka 'yan bindiga 10 a Giwa, sun ceci mutum 1

Mata 6 da kananan yara 9 sun tsero daga hannun Boko Haram
Mata 6 da kananan yara 9 sun tsero daga hannun Boko Haram. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Uku daga cikin wadanda aka sacen an kwashe su ne tare da kananan 'ya'yansu biyar yayin wani samame da 'yan ta'addan suka kai Takulashi a watan Oktoban shekarar da ta gabata.

Sauran ukun kuwa an sato su ne tare da yaransu hudu a garin Cofure a watan Mayun da ta gabata kamar yadda Zuwaira Gambo, kwasmishinan harkokin mata ta jihar Borno ta sanar, Channels TV ta ruwaito.

Wadanda aka sacen sun hada da mace mai cikin wata takwas daga Cofure wacce ta yi tafiyar kwanaki shida daga dajin Buni Yadi har zuwa garin Damboa a jihar Borno, tazarar kilomita casa'in, Gambo ta ce.

"Sun nuna karfin halinsu, tafiyar kwanaki shida a daji ba wasa ba ce," Gambo ta ce yayin gabatar da wadanda suka tsero ga Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum da shugabannin Kiristoci.

Kara karanta wannan

Zamfara: A kalla rayuka 12 sun salwanta, 'yan bindiga sun kone motar 'yan sanda

Zulum ya nuna jin dadinsa yayin karbar wadanda aka sacen inda ya ce:

"Mun gode wa Ubangiji da ya ceto ku tare da ba ku kariya daga hannun 'yan ta'adda."

Gwamnan kudu ya ce IPOB ba su kai 'yan bindiga gurbata ba, ya shirya sasanci da su

A wani labari na daban, Okezie Ikpeazu, gwamnan jihar Abia, ya ce 'yan awaren Indigenous People of Biafra (IPOB) ba su kai 'yan bindigan arewa gurbacewa ba.

A yayin tattaunawa da jaridar Vanguard, gwamnan ya ce hanyar da ta fi dacewa a shawo kan matsalar masu tada kayar bayan shi ne gwamnatin tarayya ta tattauna da su.

"Dole ne mu tattauna da IPOB. Eh, dole ne mu samu hanyar tattaunawa da su. Wadannan mutanen ba su kai wadanda ke arewa maso gabas ko arewa maso yamma fitina ba. Masu zuwa makarantu kuma su kwashe malamai da dalibai ko kuma su shiga masallaci ko coci su kwashe masu bauta," yace.

Kara karanta wannan

Boko Haram sun kashe sojoji, sun raunata janar, sun yi awon gaba da motocin soji

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: