Al Makura: Ƴan Bindiga Sun Bi Dare, Sun Sace Hadimin Tsohon Gwamna, an Bazama Daji
- Yan bindiga da ake zargin barayi ne sun kai wani hari a gidan hadimin tsohon gwamna a jihar Nasarawa
- Maharan sun sace Alhaji Adamu, mai taimaka wa tsohon gwamna Tanko Almakura, daga gidansa a birnin Lafia
- Rundunar ’yan sanda da tawagar yaki da garkuwa sun bazama domin ceto wanda aka sace tare da kama masu hannu a ciki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lafia, Nasarawa - Al'umma sun shiga wani irin yanayi bayan yan bindiga sun kai wani hari a birnin Lafia.
Majiyoyi sun ce yan bindiga da ake zargin barayi ne sun yi garkuwa da hadimin tsohon gwamnan Nasarawa, Tanko Al-Makura.

Source: Facebook
Rahoton Zagazola Makama ya ce maharan sun dauke Alhaji Adamu a jiya Juma'a 15 ga watan Agustan 2025 a jihar Nasarawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mukaman da Al-Makura ya rike a siyasa
Tsohon gwamna, Umaru Tanko Al-Makura ya mulki jihar Nasarawa daga shekarar 2011 zuwa 2019 karkashin CPC kafin a hade ta dawo APC a 2014.
Al-Makura ya kasance daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar PDP a jihar Nasarawa a 1998 shekara daya kafin dawowa mulkin dimokuraɗiyya.
A yanzu, yana daga cikin manyan jiga-jigai a APC wanda kafin nadin sabon shugaban jam'iyyar ake saka shi cikin masu neman kujerar.
Yadda yan bindiga suka sace hadimin Al-Makura
Rahoton leken asiri sun shaida cewa lamarin ya faru ne ranar Juma'a da ƙarfe 3:40 na asubahi a gidansa.
An ce harin ya faru ne a gidan wanda aka sace, da ke kan hanyar Alkali da ke Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.
"Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa wasu ne da ba a san su waye ba suka dauke mutumin ne."

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Yan bindiga sun kutsa gidan Sarki da tsakar dare, sun sace ƴaƴansa
- Cewar wata majiya

Source: Original
Jami'an tsaro sun bazama daji a Nasarawa
Majiyoyi sun ƙara bayyana cewa jami’an sintiri, tawagar yaki da garkuwa da sauran dakarun tsaro sun bazama domin bin sawun ’yan bindigar.
Hukumomi sun tabbatar da cewa ana ɗaukar dukkan matakai don ceto wanda aka sace ba tare da an cutar da shi ba da kama masu laifi.
Sai dai har zuwa wannan lokaci da ake hada rahoton babu wani sanarwa musamman daga rundunar yan sanda duk da kokarin ceto shi da wasu jami'an hadin guiwa suke yi.
Jihar Nasarawa na daga cikin jihohi da ke fama da matsalar hare-haren yan bindiga wanda ya ke jawo asarar rayuka da duniyoyin jama'a.
Nasarawa na makwabtaka da Benue da ke shan fama kan hare-haren wanda har yanzu an gagara kawo karshen lamarin.
Yan sanda sun gwabza fada da yan bindiga
Mun ba ku labarin cewa rundunar yan sandan Nasarawa ta dakile harin ƴan bindiga a hanyar Kadarko–Makurdi, inda suka tilasta musu guduwa zuwa dajin Benue.
An yi musayar wuta mai zafi, wani ɗan sanda ya ji rauni, kuma wani farar hula ya mutu sakamakon harsashin ƴan bindigar.
Kwamishinan yan sanda, Jauro-Mohammed ya ba da umarnin bincike, yana mai tabbatar wa jama'a za a kama waɗanda suka kai harin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

